Hatsarin mota: Mutane 22 sun mutu, 11 sun samu rauni a Katsina

Hatsarin mota: Mutane 22 sun mutu, 11 sun samu rauni a Katsina

Mutane ashirin da biyu, yawancinsu mata da kananan yara, sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Kafur da ke kan hanyar Kankia zuwa Danja a jihar Katsina.

Mummunan hatsarin , wanda ya faru ranar Asabar, ya ritsa da wasu motoci kirar J5 guda biyu wadanda suka yi karo. Motocin biyu na dauke da jimillar mutane 36.

Kakakin hukumar kiyaye hatsari ta kasa (FRSC) a jihar Katsina, Abubabakar Usman, ya shaida wa gidan talabijin na Channel ce wa mutane 11 sun samu rauni sakamakon hatsarin, yayin da mutane uku suka tsira babu ko kwarzane.

Motocin biyu da hatsarin ya ritsa da su, sun kama wuta nan take bayan sun yi karo da juna, lamarin da ya yi sanadiyyar konewar fasinjoji 22.

Wani shida, Shafi'u Suleiman, ya ce daga cikin mutanen da hatsarin motar ya ritsa da su akwai wata amarya da kawayenta da wasu matan aure da zasu raka ta dakin mijinta bayan kammala shagalin biki.

Hatsarin mota: Mutane 22 sun mutu, 11 sun samu rauni a Katsina
Hatsarin mota: Mutane 22 sun mutu, 11 sun samu rauni a Katsina
Asali: Twitter

A cewar shaidar, amaryar da daya daga cikin direbobin motocin, suna daga cikin wadanda suka rayu. Sai dai, hukumar FRSC ta ce ba ta tabbatar da hakan ba tare da bayyana cewa "har yanzu muna aikin ganin mun gano bayan dukkan mutanen da hatsarin ya ritsa da su".

DUBA WANNAN: Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram

"Mun dauki mutanen da hatsarin ya ritsa da su zuwa babban asibitin garin Malumfashi domin duba lafiyar wadanda suka samu rauni kafin mika su hannayen 'yan uwansu," a cewar Usman.

Kazalika, ya bayyana cewa shugabannin al'umma da malaman addini sun jagoranci binne gawar wadanda suka yi konewar da ba za a iya ganesu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel