Majalisar dattijan kasar Utah za ta halsta auren mace fiye da daya

Majalisar dattijan kasar Utah za ta halsta auren mace fiye da daya

- Majalisar dattijan kasar Utah za ta janye dokar hana karin aure

- A halin yanzu, dokar Utah ta haramta auren mace fiye da daya kuma hukuncin shekaru 5 ne a gidan yari

- Amma yanzu dokar da Henderson ke son a kafa za ta ba mazan damar auren mata fiye da daya ba tare da samun dauri ba

Majalisar dattijan kasar Utah za ta janye dokar hana karin aure. An tattauna hakan ne tare da amincewa a zauren majalisar dattijan kafin a tura wa zauren majalisar don kara tattaunawa a kai, jarida Salt Lake City Tribune ta ruwaito.

Ma'aikatar shari'a, cibiyoyin tabbatar da dokoki da kuma kwamitin zartar da hukunci ne suka tura bukatar ga majalisar.

Wanda ya dau nauyin dokar shine Sanata Deidre Henderson wanda ya ce hana karin aure a kasar tare da mayar da shi laifi yasa duk wasu laifuka da suka shafi hakan a kasar ake boyewa don gudun hukunci.

Majalisar dattijan kasar Utah za ta halsta auren mace fiye da daya
Majalisar dattijan kasar Utah za ta halsta auren mace fiye da daya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Barawo ya sace waya tare da kwashe kudin asusun bankin, ya kara da cin bashin bankin

Henderson ya ce: "Mutanen da na samu tattaunawa da su, sun bayyana cewa dokar na hana su shakatawa cikin mutane. Ana kallonsu kamar wasu na daban cikin jama'a. Suna jin kamar sun zama makaryata kuma suna koyawa 'ya'yansu karya don gujewa shari'a."

A halin yanzu, dokar Utah ta haramta auren mace fiye da daya kuma hukuncin shekaru 5 ne a gidan yari ga wanda aka kama da laifin. Akwai karin shekaru 15 ga wanda aka kama da laifin damfara, cin zarafin kananan yara, sumogal da kuma safarar mutane.

Amma yanzu dokar da Henderson ke son a kafa za ta ba mazan damar auren mata fiye da daya ba tare da samun dauri ko hukunci daga shari'a, jaridar Tribune ta ruwaito.

Masu sukar wannan bukatar ta Henderson sun hada da daraktar zabin sautika Angela Kelly, wacce ta kwatanta auren mace fiye da daya da laifi babba kuma bautarwa, in ji jaridar Tribune.

Ora Barlow, wacce ta tashi a gidan yawa ta ce ba ta bar dukiyarta ta huta ba har sai da aka zartarwa da shugabannin cocinsu hukunci.

"Akwai dalilin yin dokar kuma domin irinmu ce wadanda aka ci zarafi" Barlow ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel