Rikici: Sama da 'yan gudun hijira 8,000 ne daga kasar Kamaru suka shigo Najeriya

Rikici: Sama da 'yan gudun hijira 8,000 ne daga kasar Kamaru suka shigo Najeriya

- ‘Yan gudun hijira 8,000 ne daga kasar Kamaru suka shigo yankin Gabas da Kudancin Najeriya a cikin makonni biyu da suka gabata

- An gano cewa rikici ya barke a kasar Kamarun ne tsakanin rundunar sojin da kuma ‘yan tawaye masu son kafa gwamnatinsu

- Kamar yadda cibiyar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta tabbatar, masu gudun hijirar zasu ci gaba da shigowa Najeriya don samun mafaka

‘Yan gudun hijira 8,000 ne daga kasar Kamaru suka shigo yankin gabas da Kudancin Najeriya a cikin makonni biyu da suka gabata. A ranar Alhamis ne cibiyar kula da ‘yan gudun hijira ta karkashin majalisar dinkin duniya ta tabbatar da hakan bayan barkewar tashin hankali tsakanin jami’an tsaro da kuma ‘yan ta’adda.

A karuwar yawan ‘yan gudun hijirar da aka samu sakamakon rikicin da ya barke a yayin zaben kasar a makon da ya gabata, ‘yan gudun hijira daga kasar Kamaru sun kai kusan 60,000 a Najeriya, in ji cibiyar majalisar dinkin duniya, kamar yadda jaridar Gistmania ta tabbatar.

Rikici ya barke tsakanin rundunar sojin kasar Kamaru da kuma ‘yan tawayen kasar masu fatan kafa kasar su ta kansu mai suna Ambazonia. An fara rikicin ne bayan da gwamnatin ta tsawatarwa masu zanga-zangar lumanar a yayin da tayi korafin a kan hakan.

Rikici: Sama da 'yan gudun hijira 8,000 ne daga kasar Kamaru suka shigo Najeriya
Rikici: Sama da 'yan gudun hijira 8,000 ne daga kasar Kamaru suka shigo Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya

‘Yan ta’addan masu son kwace garin sun tirsasa miliyoyin jama’a barin gidajensu tare da gabatar da Shugaban kasa Paul Biya tare da manyan kalubalen shi tun bayan da ya hau mulki a shekaru 40 da suka gabata.

Cibiyar kula da ‘yan gudun hijiran ta majalisar dinkin duniyar ta sanar da cewa “ku tsammaci zuwan ‘yan gudun hijira saboda wasu daga cikinsu na iyakoki kuma suna kokarin shigowa Najeriya,” takardar ranar Alhamis din ta bayyana.

“An gano cewa ‘yan gudun hijirar na kusantowa inda wasu suka iso ta iyakoki dauke da raunikan da suka ji sakamakon harbin bindiga,” in ji cibiyar.

Kamar yadda sabbin ‘yan gudun hijirar suka bayyana, da yawansu sun iso ne daga yankunan da ke kusa da iyakokin kuma da kafa suka tako har cikin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel