Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta musanta zargin hannunta a garkuwa da kashe wata likita

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta musanta zargin hannunta a garkuwa da kashe wata likita

- Rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna ta musanta zargin wani jami’inta da ake da hannu cikin kisan Mrs Ataga

- An yi garkuwa da likitar a jihar Kaduna ne kuma sai aka fara yadawa cewa dan ta ya gane dan sanda daya cikin wadanda suka kashe mahaifiyar shi

- Rundunar ta ce tun bayan samun wannan labarin ta fada bincike wanda ba ta samu wani kwakwaran bayani a kai ba

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta musanta jita-jitar da ake ta yadawa na cewa daya daga cikin yaran likita Mrs Ataga da masu garkuwa da mutane ya gane fuskar wani dan sanda a cikin masu garkuwa da mutanen da suka kashe mahaifiyar shi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya ce babu dan sandan rundunar ko wani dan sanda a fadin Najeriya da ke da hannu a cikin kisan Mrs Ataga, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

‘Yan sandan sun tabbatar da cewa iyalan Ataga tuni suka musanta labaran kanzon kuregen da ke ta yawo a kafafen sada zumuntar.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta musanta zargin hannunta a garkuwa da kashe wata likita
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta musanta zargin hannunta a garkuwa da kashe wata likita
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya

Kamar yadda takardar ta bayana cewa:

1. Hankalin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kai ga wasu wallafe-wallafe da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani na hannun ‘yan sanda a sace matar Dr. Philip Ataga.

2. Rundunar na son bayyana cewa labarin bashi da tushe balle makama kuma wasu ne suka kaga shi don bata sunan rundunar. Akwai bukatar jama’a su gane cewa, iyalan Ataga sun karyata aukuwar lamarin.

3. Tun bayan da rundunar ta samu wannan labarin, ta fada bincike kuma har yanzu bata samu wani kwakwaran labari ba. Ta gano cewa an shirya ne don bata sunan rundunar.

4. Kwamshinan ‘yan sandan jihar, CP UM Muri yana kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labarin tare da kira ga cibiyoyin tsaro da su tabbatar da rahoto kafin su wallafa saboda rundunar ba za ta sassautawa duk wanda ta kama da laifin yada jita-jita ba.

An samu gawar Mrs Ataga ne a cikin dajin yankin Kakau da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan kwanaki bakwai da sace ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel