Wasu daliban Najeriya da ke China na cikin mawuyacin hali, sun yi kira ga FG

Wasu daliban Najeriya da ke China na cikin mawuyacin hali, sun yi kira ga FG

- Wasu daliban Najeriya da ke zama a Wuhan, inda cutar Coronavirus tayi Kamari sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da su kai musu dauki

- Daliban sun bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta manta dasu saboda kayayyakin kariya daga cutar nasu sun kare

- Gidan talabijin din CNN ya nemi jin ta bakin ofishin jakadancin Najeriya a birnin Beijing tare da ma’aikatar kula da harkokin waje ta Najeriya amma hakan bai yuwu ba

Wasu daliban Najeriya da ke zama a Wuhan; inda barkewar cutar Coronavirus yayi kamari a kasar China, sun zargi gwamnatin tarayya da watangarar da su.

An rufe birnin tun makonni uku da suka gabata wanda hakan yasa gwamnatin kasar ta kwashe daliban kasashen waje da ke karatu a nan, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

A yayin magana da CNN, daya daga cikin daliban mai suna Victor Vincent wanda ke karatu a jami’ar Geosciences da ke kasar China din, ya nuna damuwar shi a kan yadda gwamnati ta manta dasu.

Vincent na daya daga cikin daliban Najeriya 50 da ke rayuwa a Wuhan wanda suka zargi Najeriya da mantawa dasu duk da irin rokon da suke yi na a kwashesu sakamakon kyalesu da aka yi babu magani.

Wasu daliban Najeriya da ke China na cikin mawuyacin hali, sun yi kira ga FG
Wasu daliban Najeriya da ke China na cikin mawuyacin hali, sun yi kira ga FG
Asali: UGC

Daliban tare da malamai da ‘yan kasuwan Najeriya da ke zama a yankin Hubei din sun jima suna rubutu tare da kira ga gwamnatin Najeriya da ta tallafa musu amma har yanzu babu labari.

A yayin da cutar ta kashe sama da mutane 1,000, kasashen duniya na ta kokarin kwashe ‘yan kasarsu daga yankin amma Najeriya tayi shiru.

Vincent wanda ke daya daga cikin shugabannin daliban ‘yan Najeirya a Wuhan, ya ce kungiyarsu na kira ga gwamnatin Najerya da ta kwashesu tare da basu abubuwan bukata da suka hada da abin toshe hanci, safar hannu da sauransu.

KU KARANTA: Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya

Sun dan samu haske a ranar Alhamis da ta gabata bayan da Vincent ya karbo $2,870 wanda jakadan Najeriya a kasar China ya ba daliban. An bada wannan kudin ne don ya taimaka musu wajen samun abinci da sauran kayayyaki.

“Ban da wannan, har yanzu babu komai. Bamu san lokacin da za a kwashemu ba. A kowacce rana da ke wucewa, burin tafiyarmu na raguwa ne,” cewar dalibin da ke karatu a Wuhan tun 2018.

CNN ta dangana da son jin ta bakin ma’aikatar al’amuran kasashen waje na Najeriya da kuma ofishin jakadancin Najeriya da ke Beijing amma babu martani

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel