Shugaban EFCC ya gargadi ma’aikatan gwamnati game da zuwa aiki latti

Shugaban EFCC ya gargadi ma’aikatan gwamnati game da zuwa aiki latti

Mukaddashin shugaban kasa hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa zuwa wajen aiki ba akan lokaci ba shi ma wani nau’i ne na cin hanci da rashawa.

Daily Trust ta ruwaito Magu ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, 14 ga watan Feburairu yayin da hukumar EFCC da hukumar bautan kasa NYSC suka gudanar da tattakin hakada domin yaki da rashawa a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya ware naira biliyan 4.7 don baiwa daliban Kaduna tallafi

A yayin jawabinsa, Ibrahim Magu ya bayyana cewa makara zuwa wajen aiki nau’i ne daga cikin nau’o’in rashawa, don haka shi ma wani babban laifi ne da ya kamata a zage damtse wajen yaki da shi domin a magance shi.

“Abin takaici ne a ce karfe 10:30 na safe, amma duka duka ma’aikatan dake sakatariyar gwamnatin tarayya basu wuce kashi 10 ba, wannan ma nau’i ne na rashawa, kuma dole a yi maganin hakan.” Inji shi.

Daga cikin wadanda suka gudanar da tattakin akwai matasa masu yi ma kasa hidima dake cikin kungiyar yaki da rashawa, sai kuma wasu matasa yan bautan kasa na daban dake da ra’ayin yaki da rashawa don haka suka bayar da goyon baya.

A jawabinsa, ministan harkokin wasanni, Sunday Dare ya yi kira ga matasa dasu cigaba yaki da rashawa a duk inda suka samu kansu, tare da kira a garesu su watsa sakon yaki da rashawa da abokansu, inda ya jaddada cewa idan har aka yaki rashawa, rayuwa za ta yi kyau a kasar nan.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kaduna ta ware kimanin naira biliyan 4.7 domin daukan nauyin daliban jahar Kaduna dake karatu a kasashen waje tare da baiwa wadanda suke karatu a gida tallafi, kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana.

Shugaban hukumar Hassan Rilwan ne ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labaru a ranar Alhamis, 13 ga watan Feburairu, a garin Kaduna.

Malam Hassan ya bayyana cewa sun biya kudin tallafi ga dalibai 4,400 a cikin dalibai 7, 598, sa’annan ya kara da cewa sun tura dalibai karatu zuwa kasar Amurka, Birtaniya, Australia, Jamus da kuma Cuba.

“Daga cikin daliban akwai Abba Dauda Maitala wanda ya samu tallafin naira miliyan 15 don yin karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar tsaro na yanar gizo a jami’ar Northumbria dake garin Newcastle, Birtaniya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel