Hedkwatan tsaron Najeriya ta tona asirin wata kungiya da ke yi wa Boko Haram aiki

Hedkwatan tsaron Najeriya ta tona asirin wata kungiya da ke yi wa Boko Haram aiki

Hedkwatar tsaro ta kasa, ta kushe rahoton kwanan nan da kungiyar Amnesty International ta fitar a kan al’amuran rundunar sojin Najeriya a yankin Arewa maso gabas na kasar nan.

Kungiyar Amnesty International, wacce ta zargi rundunar sojin Najeriya da kone wasu kauyuka tare da tsare mazauna yankin, an zargeta da goyon bayan ta’addancin mayakan Boko Haram da na ISWAP, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

A takardar da mukaddashin daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu ya fitar, an zargi kungiyar da yi wa rundunar sojin Najeriya zagon kasa don taimakawa ta’addanci a yankin a yankin Arewa maso gabas.

Kamar yadda takardar ta ce: “Hedkwatar tsaro ta gano wani rahoton karya da kungiyar Amnesty International ta fitar a yunkurin ta na zagon kasa ga sojin Najeriya tare da goyon bayan ta’addancin Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso gabas.”

Hedkwatan tsaron Najeriya ta tona asirin wata kungiya da ke yi wa Boko Haram aiki
Hedkwatan tsaron Najeriya ta tona asirin wata kungiya da ke yi wa Boko Haram aiki
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ya yi karar matarsa a kotu domin ta hana shi kusantar har tsawon kwanaki 48

Ta kara da cewa, “Dole ne kungiyar ta fahimci cewa Najeriya na yaki da ta’addanci a Arewa maso gabass kuma rundunar na da hakki tun daga kundin tsarin mulkin kasar nan na kare rayuka da kadarorin ‘yan kasa. Kwashe fararen hula daga inda ake ganin hatsari ne ga rayukansu dole ne.”

“Dogaro da bayanan sirri, ana kama ‘yan ta’adda sannan a bincikesu ta hannun rundunar sojin da sauran cibiyoyin tsaro. Duk wanda aka gano bashi da hannu ana wanke shi ne tare da sallamarsa. A don haka ne ake bukatar kungiyar ta gane cewa yada wasu kalamai na karya da take yi don zagon kasa da rundunar sojin Najeriya ba za a lamunta ba.” Ta ce.

“Muna kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton kungiyar Amnesty International saboda babu gaskiya a ciki kuma ta ci karo da kokarin rundunar sojin Najeriya na yaki da ta’addanci a Arewa maso gabas.” Cewar takardar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
NDA
Online view pixel