Mutane 10 da suka fi kowa arziki a Najeriya a 2020 da kiyasin dukiyarsu (Hotuna)

Mutane 10 da suka fi kowa arziki a Najeriya a 2020 da kiyasin dukiyarsu (Hotuna)

Akwai manyan masu arziki a nahiyar Afirka da a kowacce shekara suke shiga jerin masu kudin duniya a mujallar Forbes da sauran mujallu. Najeriya kasa ce mai cike da jama’a masu tarin dukiya. Kasuwanci ne jigon arzikin mafi yawan su.

Duk da cewa kuwa, kungiyoyi da dama kan yi sharhi ko kuma bayyana mutane masu arziki, toh ba kowanne mai arzikin ake hadawa dashi ba. A kowanne shekara kuwa a kan samu sauyi a jerin masu kudin. Hakan na nuna cewa wasu na samu ne inda wasu ke tafka asara ko kuma su rasa saboda wasu dalilai. Ga jerin manyan masu kudin Najeriya da adadin dukiyarsu a 2020.

10. Fifi Ekanem Ejindu - $850 million

Fifi Ekanem mace ce mai kamar maza. An san ta ne da kamfaninta mai suna neo-traditional kuma hakan yasa ta samu lambobin yabo saboda hazakarta. Ba a nan Fifi ta tsaya ba, tana kasuwancin man fetur da iskar gas tare da dillanci.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: Depositphotos

9. Hajia Bola Shagaya - $950 million

Najeriya na da mata masu kamar maza wajen jajircewa a neman arziki. Hajia Bola Shagaya ta shiga jikin manyan bankin Unity na shekaru da dama. Kasuwancinta sun shafi kyale-kyale ne da sauransu.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: Depositphotos

8. Jim James Ovia - $980 million

Waye bai san bankin Zenith ba? Bankin na daya daga cikin manyan masana’antun kudi a Najeriya kuma Jim Ovia ne ya kirkiro shi. A matsayin shi na daya daga ciki manyan masu kudin da ya mallaki makuden kudade.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: UGC

7. Orji Uzor Kalu - $1 billion

Hamshakin mai dukiya ne amma kudinsa sun dan ragu saboda faduwar kudin gidaje da kuma man fetur.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: UGC

6. Folorunsho Alakija - $1 billion

Folorunsha Alakija ta kasance mace mai kamar maza. Kasuwancinta ya shafi man fetur da kyale-kyale. Ta bayyana a mace baka mafi arziki a duniya kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa. Ta fi kowacce mace kudi a Najeriya.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: Getty Images

5. Pascal Uzoma Dozie - $1.1 billion

Wannan dan kasuwar na daya daga cikin ‘yan kasuwa da suke da hannayen jari a bankin Diamond, Kunoch Limited da sauransu. Shine shugaban MTN a Najeriya.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: UGC

4. Jimoh Ibrahim - $1.1 billion

Jimoh Ibrahim ya samu nasarar arzikinsa ne ta hanyar sana’ar man fetur. Shi ne mamallakin Global Fleet Group. Kasuwancinsa sun hada da inshora, otal, dillanci da sauransu.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: UGC

3. Femi Otedola – 1.8 billion

Femi Otedola ne mai babban hannun jarin da ke juya kamfanin mai na Forte Oil. Arzikinsa ya matukar shahara.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: Instagram

2. Mike Adenuga - $7.2 billion

Mike sananne ba a Najeriya kadai ba, har da duniya sakamakon kamfaninsa na Globacom. Kasuwancinsa sun yawaita ne har a Afirka ta yamma.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: Depositphotos

1. Aliko Dangote - $9.9 billion

Wannan suna ba sai anyi bayani a kan shi ba. Babban dan kasuwa ne wanda ya saka hannayen jari a kasuwanci kala-kala. Shi ne bakin mutum mafi arziki a duniya baki daya.

Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Manyan masu arziki 10 a Najeriya da kiyasin dukiyarsu
Asali: Getty Images

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164