Hukumar EFCC ta kama manyan daraktoci da satar naira biliyan 700

Hukumar EFCC ta kama manyan daraktoci da satar naira biliyan 700

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kama wasu manyan daraktocin kamfanin Petro Union Oil and Gas Limited guda hudu kan zarginsu da satar zambar kudi dala biliyan 2, fiye da naira biliyan 700.

Sahara Reporters ta ruwaito an ware kudaden ne domin gina manyan matatun mai guda uku a Najeriya da kamfanin sarrafa sinadaran man fetir. Daraktocin sun hada da; Abayomi Kukoyi, Kingsley Okpala, Chidi Okpalaeze da Emmanue Okpalaeze.

KU KARANTA: Kudin makamai: Dasuki ya nemi Kotu ta ba shi izinin tafiya duba lafiyarsa a kasar waje

Sauran sun hada da Isaac Okpala wanda ya mutu, da kuma Gladys Okpalaeze, wanda ake nemanta har yanzu ba’a kamata ba.

Lauyan EFCC, Rotimi Jacobs ya bayyana cewa a ranar 29 ga watan Disambar 1994 da shekarar 2007 aka aikata laifin a jahar Legas, a cewarsa laifin da daraktocin suka aikata ya saba ma sashi na 1(2)(a) na kundin hukunta laifuka na Najeriya.

Sai dai dukkaninsu sun musanta aikata wani laifi, daga nan sai Alkalin kotun, mai sharia Liman ya bada umarnin cigaba da rikesu a hannun EFCC, sa’annan ya sanya ranar 19 ga watan Feburairu domin yanke hukuncin game da bukatar neman beli da suka mika masa.

Bugu da kari hukumar EFCC ta kama wasu mutane 15 da laifin zamba cikin aminci a unguwar Alafara na garin Ibadan a jahar Oyo da suka hada da: Olanrewaju Olatunji, Femi Olatunji, Abiodun Ojo, Lawal Ahmed, Adedeji Olatunbosun, Adeniyi Ramon da Oladipupo Oluwatobilola.

A wani labarin kuma, Akalla mutane biyu ne suka samu munana rauni sakamakon barkewar rikicin kabilanci tsakanin yan kabilar Hausa da kabilar Yarbawa dake kasuwanci a kasuwar Lafenwa dake garin Abekuta, babban birnin jahar Ogun.

Rikicin ya faru ne a daren Laraba, 12 ga watan Feburairu, kuma ya samo asali ne bayan samun jita jitan mutuwar wani dan kasuwa bahaushe wanda ake zargin masu karbar kudin harajin kasuwa ne suka sare shi.

Majiyarmu ta ruwaito wani dan kasuwa Bahaushe ne ya ki biyan harajin da ake biyan yan iskan gari zauna gari banza a kullum bayan kwashe kusan sa’o’i 10 yana cin kasuwa, hakan ne ya tunzura zauna garin banzan suka sassare shi.

Ganin barnar da suka yi masa ne sai suka ranta ana kare, suka barshi kwance male male cikin jini, rai a hannun Allah. Sai dai mai magana da yawun Yansandan jahar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace babu wanda ya mutu a rikicin

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng