Rashin tsaro: Mutane 3188 aka kashe a Najeriya a shekarar 2019 - Lissafi

Rashin tsaro: Mutane 3188 aka kashe a Najeriya a shekarar 2019 - Lissafi

Akalla yan Najeriya 3188 aka yiwa kisan gilla a shekarar 2019 sakamakon rashin tsaron da ya addabi dukkan sassan kasar, wani rahoton lissafi ya bayyana bayan bibiya da tattara kashe-kashen da suka faru.

A cewar kungiyar 'Nigeria Mourns', mutane 3188 aka kashe tsakanin Junairu da Disamban 2019 a lamuran rashin tsaro irinsu garkuwa da mutane, Boko Haram/ISWAP, yan bindiga, yan baranda da sauran su.

A cewar rahoton, cikin wadannan mutanen da aka kashe 2707 masu farin hula ne, yayinda 481 jami'an tsaro ne.

Wannan na nufin cewa cikin kowani mutane biyar da aka kashe, akwai jami'in tsaro daya.

Rashin tsaro: Mutane 3188 aka kashe a Najeriya a shekarar 2019 - Lissafi
Rashin tsaro: Mutane 3188 aka kashe a Najeriya a shekarar 2019 - Lissafi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Fill-filla: - Yadda zababben mataimakin gwamna ya janyowa maigidansa da APC gaba daya asara

Jihar da kashe-kashen ya fi shafa bisa rahoton itace jihar Borno a Arewa maso gabas, sannan jihar Zamfara.

Kungiyar ta kara da cewa wannan adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu ne ba wadanda suka bace ba.

"Bayan kwashe shekara daya muna bibiyan rikice-rikice da rubuta rayukan da aka rasa, mun samu mutuwa 3188 a shekarar 2019"

"Yayinda muke bibiyan kashe-kashen, mun fuskanci yadda ake yawaita kashe jami'an tsari sannan a tafi makamansu."

"Wani abin mamaki shine akwai wurare da dama a Arewacin Najeriya da aka manta da su sannan garuruwan da rafuka suka mamaye a kudu maso kudancin Najeriya inda yan bindiga suka maishe dabarsu." Kungiyar ta bayyana a ranar Alhamis.

Mun kawo muku a baya cewa Akalla mutane 245 suka rasa rayukansu a watan farkon shekarar 2020, rahotannin kashe-kashe da aka tattara ya bayyana hakan.

A cewar rahoton bincike da InterNations ta gudanar, Najeriya ce kasa mafi hadarin zama a duniya na uku bayan kasar Afghanistan da Syriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng