Mutumin kasar Netherlands da ya fi kowa tsanar Musulunci a duniya ya Musulunta

Mutumin kasar Netherlands da ya fi kowa tsanar Musulunci a duniya ya Musulunta

- Wani fitaccen dan siyasa a kasar Netherlands mai suna Joram Van Klaveren ya Musulunta, lamarin da ya bawa kowa mamaki kenan

- Van Klaveren dai yana daya daga cikin wadanda basa kaunar addinin Musulunci a rayuwarsu, inda har ya taba kiran littafin Al-Qur'ani mai girma da guba

- To sai dai kuma abin mamaki Joram ya Musulunta ne a lokacin da yake rubuta wani littafi da yake nuna kiyayya ga addinin Musulunci

Wani babban dan siyasa na kasar Netherlands, wanda yake tsohon makiyin addinin Musulunci ne, ya bayyana cewar ya karbi kalmar Shahada.

Mutumin mai suna Joram Van Klaveren ya taba cewa Musulunci karya ne kuma Al-Qur’ani guba ne, ya fadi hakan ne a lokacin da yake tashen siyasa a jam’iyyar PVV ta kasar.

Sai dai kuma dan siyasar mai shekaru 40 a duniya ya dawo addinin Musulunci a lokacin da yake rubuta wani littafi na nuna kiyayya ga Musulunci.

KU KARANTA: Yadda rayuwata ta sauya sanadiyyar haduwa ta da Zulum - Malamar Firamare Obiageli

Mr Van Klaveren dan majalisa ne a jam’iyyar PVV wanda ya hau kujera daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2014.

A wata hira da gidan jarida na Jaridar Dutch suka yi dashi, Mr Van Klaveren, ya ce maganganun da yayi a baya game da Musulunci rashin sani ne.

Inda ya danganta maganar tashi da alaka da jam’iyyar da yake ta PVV, wacce dokar ta shine duk abinda bai yi daidai ba to yana da alaka da Musulunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel