An kuma: Wata mata ta caki mijinta har lahira

An kuma: Wata mata ta caki mijinta har lahira

- Wata mata ta soki mijinta mai suna Daniel da wuka har lahira a jahar Rivers

- An tattaro cewa lamarin ya afku ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu

- Makwabcin mutumin ne ya wallafa a shafinsa na zumunta

Wani mummunan lamari ya afku a Port Harcourt, babbar birnin jahar Rivers inda wata mata ta soki mijinta mai suna Daniel da wuka.

An tattaro cewa lamarin ya wakana ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu.

Kamar yadda shafin Lindaikeji ta kawo wani mai amfani da shafin Facebook Iykechukwu Ikechukwu wanda ya wallafa bidiyon inda lamarin ya faru, ya yi ikirarin cewa mutumin bai taba cin amanar matarsa ba illa kawai ya kan yi mata wa’azin ta shiryu.

A cewarsa an kama wacce ta aikata laifin.

An kuma: Wata mata ta caki mijinta har lahira
An kuma: Wata mata ta caki mijinta har lahira
Asali: UGC

Ya rubuta:"Matar makwabcina ta soke shi da wuka, Allah ya ji kan ka, mutumin kirki...Mu kan yi wasan barkwanci a kullun idan muka dawo daga aiki...chioo ba zan sake ganinka ba..

"Kada wanda ya ce wani abu a kan mutumin kirki na cin amana, baya cin amana, jiya ya yi wa matarsa wa’azi kan ta shiryu amma sai ta kashe shi cikin dare."

A gefe guda mun ji cewa wata mata mai tsananin kishi ta soki mijinta da wuka har sau biyu a yayin da yake bacci saboda zargin shi da take da ajiye karuwa a waje.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ba za a taba rantsar da Diri a matsayin gwamnan Bayelsa ba - Oshiomhole

Kamar yadda mawallafin a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Chinonso Chibuogwu ya wallafa, ya ce lamarin ya faru ne a Owerri jihar Imo.

Mijin wanda aka sokawa wukar kuwa abokin shi ne. Ya ce wanda abin ya faru da shi kuwa sunan shi jude Mmadu. Kuma matar shi din ta zarge shi ne da cin amanarta shiyasa ta soka mishi wuka har sau biyu a yayin da yake bacci.

Kamar yadda jaridar Gistamania ta ruwaito, bayan tashin shi ne firgice ya samu ya tsere tun kafin ta samu nasarar ci gaba da raunata shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel