Gwamnatin Buhari ta canzawa ma’ikatan gidajen gyara-hali kayan aiki

Gwamnatin Buhari ta canzawa ma’ikatan gidajen gyara-hali kayan aiki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake ma jami’an hukumar gidajen gyaran halayya na Najeriya kayan aiki, watau Khakin da suke sanyawa a duk lokacin da suke bakin aiki.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito gwamnati ta bullo da wannan sabon sauyi ne domin ya yi daidai da sabon tsarin hukumar bayan an sauya mata suna daga hukumar kula da gidajen yari zuwa hukumar kula da gidajen gyara-hali.

KU KARANTA: Ta leko ta koma: Kalli yadda gwamnan APC ke shirin karbar mulki kafin kotu ta kwace kujerarsa

Shugaban hukumar, Jaafaru Ahmed ne ya bayyana haka a yayin da yake kaddamar da wani katafaren gini, sashin kula al’amurar mulki na makarantar gyara hali ta kasa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.

“Nan bada jimawa ba zaku gammu cikin sababbin Khakin mu, sama da shekara 100 kenan muke sanya wannan khakin, don haka akwai bukatar canza shi domin ya dace da sabon tsarin aikinmu.

“Muna kuma kokarin ganin mun tabbatar da aiwatar da sabon tsarin aikin, amma matsalar ba’a sa tsarin a cikin kasafin kudin bana, amma da zarar an samar da kasafin kudin, zamu samu daman aiwatar da dukkanin tsare tsaren don yin ayyukanmu yadda ya kamata.” Inji shi.

Jafaru ya kara da cewa a shirye su ke su kula da walwalar jami’ansu domin su ji dadin gudanar da aikinsu yadda ya kamata, ta hanyar samar musu da muhallai masu kyau da kuma biyansu albashi a kan kari.

“Muna sane da jami’an dake kula da masu laifi, saboda a daidai lokacin da muke tunanin samar da matsuguni masu kyau tare da kula da walwalar wadanda suke tsare, muna da burin samar da muhallai masu kyau ga jami’anmu tare da basu daman karo karatu.” Inji shi.

Ita ma a nata jawabin, shugabar kungiyar matan hafsoshin hukumar, PROWA, Gwamma Ahmed ta bayyana cewa kungiyarsu ta kafa wasu makarantu a sassan kasar nan baya ga babbar makarantarsu dake Abuja.

Sa’annan ta yi alkawari za su tabbata makarantar ta zama kan gaba wajen bayar da sahihin ilimi ta yadda dalibanta za su taimaka wajen ciyar da kasa Najeriya gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel