Dan takarar shugaban kasar Amurka ya zabi Musulmi ya shugabanci yakin neman zaben shi

Dan takarar shugaban kasar Amurka ya zabi Musulmi ya shugabanci yakin neman zaben shi

- Dan takarar shugaban kasar Amurka, kuma Sanata na yanzu Bernie Sanders ya bayyana Faiz Shakir a matsayin wanda zai shugabanci yakin neman zaben shi a shekarar 2020

- Faiz wanda ya kasance Musulmi ne dan asalin kasar Pakistan, lauya ne, kuma shine mai bawa Nancy Pelosi shawara wacce take shugabar masu rinjaye a majalisar kasar ta Amurka

Jim kadan bayan bayyana shi a matsayin dan takarar shugaban kasar Amurka a shekarar 2020, Sanatan kasar Amurka, Bernie Sanders ya bayyana Faiz Shakir, a matsayin mutumin da zai jagoranci yakin neman zaben shi. Jaridar Anadolu Agency ta ruwaito.

Shakir wanda yake Musulmi ne kuma lauya, Sanatan ya bayyana shi a matsayin wanda zai jagoranci yakin neman zaben na shi.

Dan takarar shugaban kasar Amurka ya zabi Musulmi ya shugabanci yakin neman zaben shi
Dan takarar shugaban kasar Amurka ya zabi Musulmi ya shugabanci yakin neman zaben shi
Asali: Facebook

Ya kammala karatunshi a jami’ar Havard, Shakir wanda yake dan shekara 39 kuma dan asalin kasar Pakistan, yayi mai bada shawara na musamman ga shugaban masu rinjaye na Sanatocin kasar ta Amurka, Harry Reid, haka kuma yanzu shine yake bawa Nancy Pelosi shawarwari, shugabar masu rinjaye ta majalisar kasar.

Sanders, wanda yana daya daga cikin mutanen da suka kawowa Hillary Clinton matsala a takarar da ta fito na kujerar shugaban kasa a shekarar 2016, ya shiga cikin jerin mutanen da za a gwabza da su a zaben da za a gabatar na shekarar 2020.

KU KARANTA: Ran maza ya baci: Hatta jihar Legas akwai Boko Haram - Buratai ya mayar da martani kan harin Boko Haram

Zaben shugaban kasar wanda za a gabatar da shi a ranar 3 ga watan Nuwambar 2020, zai zama zabe na 59 a tarihin kasar.

‘Yan Amurka za su zabi wadanda za su zaba musu shugaban kasa da kuma mataimaki, kamar dai yadda suka saba gabatarwa.

Ana sa ran za a gabatar da zaben fidda gwani a jam’iyyun na kasar Amurka a watanni shida na farkon wanan shekara ta 2020.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, wanda ya lashe zabe a shekarar 2016, ana sa ran zai sake fitowa takara a karo na biyu.

Duk wanda ya lashe zaben na shekarar 2020, za a rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2021.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel