Bayan martanin da Diri na PDP yayi, ya kama hanyar Yenagoa don rantsarwa

Bayan martanin da Diri na PDP yayi, ya kama hanyar Yenagoa don rantsarwa

- Sanata Duoye Diri yayi martani a kan nasararsa a kotun koli a yau Alhamis, 13 ga watan Fabrairu

- A takaitaccen sakon da Sanatan ya wallafa a shafinsa na Facebook, Diri ya rubuta: “Da Ubangiji muka dogara”

- A jihar Bayelsa kuwa, magoya bayan Diri sun shiga shagali da bidiri a kan tituna sakamakon hukuncin kotun kolin

Sanata Duoye Diri ya yi martani a kan nasararsa a kotun koli a ranar Alhamis 13 ga watan Fabrairu, 2020.

Diri, wanda a halin yanzu Sanata ne wanda ke wakiltar jihar Bayelsa ta tsakiya, ya samu damar bayyana a matsayin halastaccen gwamnan jihar Bayelsa bayan hukuncin kotun koili a yau.

Diri wanda ya dinga samun baki daga Abuja, a halin yanzu yana kan hanyarsa ta zuwa Yenagoa don rantsar da shi a ranar Juma’a, 14 ga watan Fabrairu 2020.

A takaitaccen martanin da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Diri ya rubuta; “Da Ubangiji muka dogara”.

Bayan martanin da Diri na PDP yayi, ya kama hanyar Yenagoa don rantsuwa
Bayan martanin da Diri na PDP yayi, ya kama hanyar Yenagoa don rantsuwa
Asali: Facebook

Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau Alhamis ne kotun koli ta kwace kujerar zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon da kuma abokin tafiyarsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, wadanda suke ta shirye-shiryen karbar rantsuwar hayewa karagar mulkin jihar.

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

Alkalai biyar na kotun, wadanda suka samu shugabancin Mai shari'a Mary Peter-Odili, sun umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta janye shahadar hayewa kujerar jagorancin jihar da ta mikawa 'yan takarar jam'iyyar APC din a jihar, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Duba da wannan kalami kuwa, jam'iyyar PDP ce za ta amshe wannan kujerar don ci gaba da mulkin jihar ta Bayelsa.

Mai shari'a Ejembi Ekwo, wanda ya karanto hukuncin kotun kolin, ya bada wannan umarnin ne bayan da aka bayyana rashin cancantar mataimakin David Lyon, Degi-Eremienyo a tsayawa takarar zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel