Tsoron kamuwa da Coronavirus ta sa an hana Odion Ighalo fara aiki cikin 'Yan wasa

Tsoron kamuwa da Coronavirus ta sa an hana Odion Ighalo fara aiki cikin 'Yan wasa

Ana rade-radin cewa an hana Odion Ighalo shiga cikin filin horaswan Manchester United, saboda tsoron yiwuwar ace ya na dauke da kwayar cutar Coronavirus.

Manchester United ta karbo aron Odion Ighalo ne daga kungiyar Shanghai Shenhua ta kasar Sin, inda wannan cuta ta fito. Yanzu dai cutar ta shiga wasu kasashen Duniya.

An ba sabon ‘Dan wasan gaban umarni ya yi atisayensa ne a wajen filin AON da sauran ‘Yan wasa su ke aiki. An yi wannan ne saboda kare yiwuwar barkewa da cutar.

Rahotannin News Telegraph sun bayyana cewa tsohon ‘Dan wasan na Super Eagles ya na aiki ne shi kadai tare da Mai horas da shi a maimakon tare da Abokan aikinsa.

KU KARANTA: Man City ta sha da kyar a hannun Manchester United

Tsoron kamuwa da Coronavirus ta sa an hana Odion Ighalo fara aiki cikin 'Yan wasa
Manchester United ta karbo aron Odion Ighalo daga Shanghai
Asali: UGC

Haka zalika Ighalo bai bi Tawagar Manchester United zuwa kasar Sifen kwanakin baya ba. An dauke ‘Yan wasan kungiyar daga Ingila ne domin a samu saukin sanyi.

Ana hana mutanen da su ka ziyarci kasar Sin (China) a cikin ‘yan kwanakin bayan nan shiga kasashen ketare. Ana sa rai hakan zai rage kamuwa da wannan cuta.

Kungiyar Manchester United ta kara daukar matakin rigakafi bayan da ta tsare Odion Ighalo mai shekaru 30, ana horas da shi kadai ba tare da sauran ‘Yan wasa ba.

Cutar Coronavirus da ake gudu, ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 1, 100 a Duniya. Sai dai ko da ya ke Sin, Ighalo bai taka kafa zuwa ainihin Garin Wuhan ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel