Ta leko ta koma: Kalli yadda gwamnan APC ke shirin karbar mulki kafin kotu ta kwace kujerarsa
Duniya makwanta rikici, kamar yadda masu iya magana suke fadi, wani sabon gwamnan jam’iyyar APC dake jiran gado a jahar Bayelsa ya ga rashi ya ga samu, yayin da kotun koli ta tsige shi ana gobe bikin rantsar da shi.
A ranar Alhamis, 13 ga watan Feburairu ne kotun kolin Najeriya ta soke nasarar da dan takarar gwamnan jahar Bayelsa a jam’iyyar APC ya samu, David Lyon tare da mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremioyo.
KU KARANTA: Yan siyasa ne suka biya ‘zauna gari banza’ don su yi ma Buhari ihu a Borno – Garba Shehu
Sai dai jim kadan kafin samun wannan hukunci, an hangi gwamnan tare da mataimakinsa suna gudanar da shirye shiryen rantsaarwarsu da a da za’a gudanar da shi a ranar Asabar, 15 ga wata, inda gwamnan ya shiga mota tare da jami’an tsaro a filin wasa na jahar yana gwajin yadda taron rantsarwar za ta kasance.
Gwamnan ya yi gwajin shiga motar rantsarwa, ya yi gwajin yadda zai tsaya kikam yayin da Yansanda suke masa faretin ban girma, ya yi gwajin yadda zai zagaya filin a cikin motar rantsarwa har ma yana kujeru bai-bai tare da jinjina da godiya, ashe ashe duk ba zata kai ga haka ba, duniya kenan.
Alkalin kotun koli da ya karanta hukuncin da kotun ta yanke, mai sharia Ejembi Ekwo ya bayyana cewa kotun ta soke nasara Lyon ne sakamakon mataimakinsa Biobarakuma ya mika ma hukumar INEC takardun bogi gabanin tsayawa takara a zaben daya gudana a ranar 16 ga watan Nuwamba.
PDP ce ta shigar da karar dan takarar mataimakin gwamnan gaban kotun, don haka kotun ta bayyana cewa tun da har ya gabatar da takardun bogi ga INEC, toh rashin gaskiyarsa ta shafi nasarar maigidansa gaba daya, saboda haka ta haramta zaben da suka ci gaba daya.
Dama a ranar 12 ga watan Nuwambar 2019 wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta haramta ma Degi takara, amma sai ya daukaka kara. Daga karshe Alkalin ya umarci INEC ta mika takardar nasara ga dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP, kuma ta bada umarnin a rantsar da shi a ranar Asabar, 15 ga wata.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng