Zulum ya ziyarci mutane 5 da suka jikkata a harin da Boko Haram ta kai jiya (Hotuna)

Zulum ya ziyarci mutane 5 da suka jikkata a harin da Boko Haram ta kai jiya (Hotuna)

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a daren Laraba ya ziyarci wadanda harin Boko Haram ya shafa a Jiddari Polo da hanyar Damboa.

Hanyar Damboa na tsakiyar birnin Maiduguri.

Daya daga cikin rokokin da yan ta'addan suka harba ta dira kusa da gidan shahrarren bilioniya, kuma Surikin Buhari, Alhaji Mohammed Indimi.

Rokan jikkata kananan yara biyar kuma na garzaya da su asibiti.

Zulum ya ziyarci mutane 5 da suka jikkata a harin da Boko Haram ta kai jiya (Hotuna)
Zulum
Asali: Facebook

KU KARANTA: Babu wanda ke tsangwaman Yari - Shugaban APC na bangaren Kabiru Marafa

Zulum ya ziyarci mutane 5 da suka jikkata a harin da Boko Haram ta kai jiya (Hotuna)
Mara lafiya

Mun kawo muku rahoton cewa akalla mutane biyar sun jikkata yayinda Boko Haram sukayi kokarin shiga Maiduguri jiya bayan zuwan shugaba Muhammadu Buhari jihar.

An tattaro cewa yan ta'addan sun shiga garin Maiduguri ne bayan Sallar Isha ta Addawari, unguwar Jiddari Polo inda suka harba roka da ya jikkata mutane 5.

Wani mazauni, Ali Maji Bukar, ya bayyana cewa na garzaya da wadanda suka raunata Asibitin jihar domin jinya.

"Bamu san abinda ya faru ba. Sai muka fara jin harbe-harbe a bayan gari da kuma hanyar Damboa." Yace

Sanda Bunu, wanda mazaunin Jiddari Polo ne ya ce bai ka yan ta'addan ba amma ya riga harsasai na yawo a sama.

"Jami'an tsaro sun zaburo da wuri kuma suka kawar da yan ta'addan amma har yanzu mutane na bakin hanya." Yace

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel