Mutane biyu sun ga ta kansu yayin da aka kama su lokacin da suka yiwa wata mata karfa-karfa suka kwace mata jariri

Mutane biyu sun ga ta kansu yayin da aka kama su lokacin da suka yiwa wata mata karfa-karfa suka kwace mata jariri

- Wasu masu satar mutane sun kuwa rasa ransu a jihar Ondo bayan da suka yi yunkurin kwatar yaro daga mahaifiyar shi

- Kamar yadda jama’ar yankin suka sanar, mahaifiyar tayi ihu ne bayan da suka kai wa yaron sura daga bayanta

- Tuni aka kama su tare da yi musu tsirara don a kona su, amma sai basaraken yankin ya dakatar dasu tare da mika wa ‘yan sanda mutane biyun

Wasu masu satar mutane guda biyu a jihar Ondo sun kusa haduwa da ajalinsu bayan sun yi yunkurin kwace yaro mai shekaru biyu daga hannun mahaifiyar shi.

A ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan jihar ondo ta kama wasu mutane biyu a yankin Erusu-Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta arewa maso yamma a jihar, bayan da suka yi yunkurin kwace yaro daga hannun mahaifiyar shi.

Mutane biyu sun ga ta kansu yayin da aka kama su lokacin da suka yiwa wata mata karfa-karfa suka kwace mata jariri
Mutane biyu sun ga ta kansu yayin da aka kama su lokacin da suka yiwa wata mata karfa-karfa suka kwace mata jariri
Asali: Facebook

Kamar yadda mahaifiyar yaron ta sanar, masu satar mutanen sun biyo ta ne tun daga yankin Aga na birnin. Daga nan ne suka yi yunkurin kwace yaron daga bayanta amma sai ta kurma ihun da ya jawo mutane.

Kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito, wani ganau ba jiyau ba ya ce ihun mahaifiyar yaron ce ta jawo hankulan mutane inda suka kai mata dauki a wajen da abun ke faruwa. Daga nan ne kuwa suka damke masu satar mutanen bayan sunyi yunkurin gudu.

KU KARANTA: An kuma: Matar aure ta cakawa mijinta wuka a yayin da yake bacci, bayan ta zarge shi da kwanciya da wata a titi

An yi wa mutanen tsirara kuma fusatattun mutanen yankin sun yi yunkurin banka musu wuta. Amma shigar basaraken yankin mai suna Oba Sunday Mogaji ne ya hana.

Daga nan ne aka mika mutanen hannun ‘yan sandan da ke yankin Oke Age. Bayan an tuhumesu ne aka gano cewa wadanda ake zargin asalin ‘yan Oyin Akoko ne amma suna rayuwa a Oke Agbe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel