Zaku fada cikin babban 'garari' matukar baku bawa gwamnati goyon baya ba - Buhari ya fada wa matasa

Zaku fada cikin babban 'garari' matukar baku bawa gwamnati goyon baya ba - Buhari ya fada wa matasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce matasa na saka rayuwarsu cikin garari ne matukar basu ba gwamnati hadin kai. Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin da yaje ta'aziyya jihar Borno inda aka kashe kusan mutane 30 a ranar Lahadi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Buhari ya ce matasa ne suka fi yawa a kasar nan kuma dole ne su taimakawa gwamnati don ganin daidaituwar kasar nan.

"Muna da matasa masu matukar fushi a Najeriya. Jimillar yawan 'yan Najeriya, matasa ne suka kwashe kashi 60 daga ciki," ya ce.

"Kuma ya zama tilas mu dinga tunatar da su cewa su zasu taimaka mana wajen samun daidaituwar kasar nan saboda gobensu tayi kyau. Idan ba zasu hada kai da gwamnati ba, gobensu ce ba za ta yi kyau ba.

"Na riga na kai shekaru 77, shekaru nawa nake tsammanin zan kara?" a cewar shi.

Zaku fada cikin babban 'garari' matukar baku bawa gwamnati goyon baya ba - Buhari ya fada wa matasa
Zaku fada cikin babban 'garari' matukar baku bawa gwamnati goyon baya ba - Buhari ya fada wa matasa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon tsiraici: Kungiya ta kare Sanata Uba Sani

Buhari ya kara da cewa, yana mamakin yadda mayakan Boko Haram suka kai har yanzu.

"A matsayi na shugaban kasa, nayi kamfen a 2015 da kuma shekarar da ta gabata cewa zan mayar da hankali kan abubuwa uku ne da suka hada da tsaro a ciki. Mulki baya yuwuwa matukar babu tsaro. Kowa ya san hakan, koda kuwa bai je makaranta ba," ya ce.

"Wadannan mayakan Boko Haram din ba zai yuwu su shigo Maiduguri ba, ba tare da hadin bakin 'yan yankin ba. A tunani na da kuma fahimtar al'adunmu da nayi, ina ta mamakin yadda har yanzu akwai Boko haram.

"Muna iyakar bakin kokarinmu a kasar nan. Har yanzu muna fama da rashin tsaro amma na san ya ragu. Ina kira ga jama'ar jihar nan da su bada hadin kai ga hukumomin tsaro mu fatattaki Boko Haram. Daga nan ne zamu iya komawa asalin mahaifarmu mu zauna." In ji Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel