Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi

Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi

- Wani mutum mai suna Michael Askham ya kashe kan shi tare da bada wasiyya mai fatan ko gwamnatin Ingila za ta canza wata doka

- Tun a watan Oktoba ne na 2018 aka gano yana dauke da cutar Motor Neurone wacce ba za ta bar shi ya tashi ba ko samun sauki

- Ya nuna damuwarshi ta yadda kasar ba ta amince wani ya taimaka mishi ba wajen kashe kan shi don rangwantawa iyalan shi dawainiyar da suke yi dashi

Baya iya tafiya ko magana da ‘ya’yan shi, Michael Askham ya yanke shawarar kashe kanshi duk da cewa kuwa ya san mutuwar zai yi komai dadewar da zai dauka yana jinya.

Michael Askham mutum ne mai shekaru 59 kuma an gano cewa yana fama da cutar motor neurone tun a watan Oktoba na 2018. Tsohuwar ma’aikaciyar jinyar ta sakankance cewa matukar bai yi wani abu a kai ba yanzu, toh zai mutu ne ta hanyar kasa hadiyar komai wanda yawun bakin shi ne zai kashe shi.

Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi
Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi
Asali: Facebook

A lokacin da Michael ke kwance yana jinya, yayi kira a kan a halasta taimakawa wajen kashe majinyaci matukar an san ba zai tashi ba. A cewar shi, hakan zai saukakawa matarshi da yaran shi biyu wahalar da suke tayi a kan shi.

“A kullum fatana in mutu kamar yadda mahaifina ya mutu a saukake,” Michael ya sanar da jaridar The Independent a yayin da suke hirantawa ta yanar gizo.

Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi
Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi
Asali: Facebook

“In je aiki, in dawo, in kwanta sai in mutu ta hanyar ciwon zuciya na farat daya. Ganin yadda karfina yake karewa kuma iyalina na fama dani baya min dadi. A hankali rayuwata take tafiya. Bana iya komai kuma bana jin dadin rayuwar.”

KU KARANTA: Allah Sarki: Bidiyon yadda wani mutumi ya fashe da kuka bayan matarshi ta gudu wajen sabon saurayinta ta bar shi da yara miskinai guda 4

A karkashin dokar Ingila da Wales a yanzu, hukuncin shekaru 14 ne ga duk wanda ya taimakawa wani ya kashe kanshi. A kowanne mako ana samun masu tafiya har zuwa Switzerland don kashe kansu.

Idan da an canza dokar, za ta bar iyalan Michael, masu kula dashi a asibiti ko kuma masu bashi magani da su bashi abinda zai kasha shi a hankali.

Kotun daukaka kara ta hana damar kara duba wannan dokar ta taimakawa wanda ke fama da matsananciyar jinya wacce ba ta tashi ba, ya karasa kanshi ko kuma wani ya taimaka mishi wajen kashe kanshi.

Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi
Babbar magana: Wani mutumi ya daina ci da sha, ya ce yana so yaga yadda yunwa za ta kashe shi
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel