Hotuna: Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja

Hotuna: Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja

- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci bude wani gidan siyar da abinci a Abuja

- An wallafa wannan sanarwar ne shafin shi na Facebook, inda aka ce gidan cin abincin mai suna Moa na nan a unguwar Maitama ne

- Wannan lamarin kuwa ya ja ake ta cece-kuce na cewa ko ikirarin gwamna Ganduje na cewa yayi wa tsohon sanatan ritayar siyasa ce ta tabbata

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanata na jhar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya jagoranci bude wani gidan siyar da abinci mai suna Moa Restaurant a unguwar maitama da ke babban birnin tarayya.

Sanata Kwanskwaso ya bayyana hakan ne shafin shi na Facebook wanda Saifullahi Hassan ke kula da shi.

Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja
Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja
Asali: Facebook

Kamar yadda ya wallafa, “A yau Laraba ne jagoran Kwankwasiyya da sauran mambobin darikar Kwankwasiyya suka jagoranci bude gidan cin abincin Moa da ke unaguwar Maitama a babban birnin tarayya da ke Abuja.”

Sai dai, wannan lamarin na faruwa ne bayan makonni biyu da Gwamna Ganduje ya bugi kirji yace yayi wa Rabiu Musa Kwankwaso ritayar siyasa, kamar yadda jaridar Labarai 24 ta ruwaito.

Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja
Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja
Asali: Facebook

Kamar yadda mai magana da yawun Gwamna Ganduje, Abba Anwar ya fitar, ya ce jam’iyyar PDP da tsohon Gwamnan da ke jagorantarta a jihar Kano sun kasa tabuka abun a zo a gani.

KU KARANTA: Hotuna: Daliban makarantar firamare sun je har gida sun ciccibo dan ajinsu da baya son zuwa makaranta

Kamar yadda kowa ya sani, dangantaka dai na ci gaba da tsami tsakanin Sanata kwankwaso da kuma Gwamna Ganduje bayan zaben da aka gudanar na 2019.

Bayan nasarar da Ganduje ya samu a kotun koli, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana nasarar da jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta samu a zaben maye gurbin da aka kammala a jihar a matsayin alama da ke nuna cewa an yi wa tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso ritaya daga siyasa.

Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja
Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja
Asali: Facebook

Sanarwar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar Juma'a ya ce gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke maraba da Kakakin majalisar jihar, Abdulaziz Gafasa da wasu manyan masu rike da mukamai a majalisar da suka raka sabbin 'yan majalisun jihar hudu zuwa gidan gwamnati.

Haka kuma a jiya muka kawo muku yadda Kwankwaso da Abba suka fito suka bayyana dalilin da ya sanya basu tarbi wannan matashin saurayin da yayi tattaki daga garin Katsina zuwa Kano ba, domin yayi musu jaje akan rashin nasarar da suka yi a kotun koli kwanakin da suka gabata.

Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja
Bayan rashin nasara a kotu, Kwankwaso ya bude gidan abinci a Abuja
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel