Hotuna: Daliban makarantar firamare sun je har gida sun ciccibo dan ajinsu da baya son zuwa makaranta

Hotuna: Daliban makarantar firamare sun je har gida sun ciccibo dan ajinsu da baya son zuwa makaranta

- Wani bidiyo da ke tashe kwanan nan a yanar gizo shine na wani dan makaranta da aka kai shi ta karfi da yaji

- Ma’abocin amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Chukwunonso Peter ne ya wallafa labarin

- Peter ya bayyana cewa yaron baya son zuwa makaranta ne duk da ana biya amma sai abokan shi suka zo suka dauke shi ta dole

Kusan a ko ina yanzu, kai ya waye kuma an gano cewa ilimi shine gishirin zaman duniya. Rashin ilimi kuwa babbar illa ce ga rayuwar dan Adam.

Wannan kuwa yasa iyayen zamanin nan basu wasa da ilimin yaransu. Koda gida ba a ci bane, toh zasu tattara su kai makaranta don ana fatan samun rayuwa mai inganci kuma cike da walwala a nan gaba.

Hotuna: Daliban makarantar firamare sun je har gida sun ciccibo dan ajinsu da baya son zuwa makaranta
Hotuna: Daliban makarantar firamare sun je har gida sun ciccibo dan ajinsu da baya son zuwa makaranta
Asali: Facebook

Bidiyon wani karamin yaro a Enugu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani. Yaron kamar yadda aka bayyana, baya kaunar zuwa makaranta ko kadan amma mahaifinshi na iya kokarin shi wajen tabbatar da cewa ya biya kudin makarantar.

KU KARANTA: Wutar Lantarki ta manya ce kawai a kasar nan talakawa sai dai hakuri - Mele Kyari

Hakazalika, yaron yakan gudo gida koda kuwa lokacin tashi makarantar bai yi ba. Hakan ce kuwa ta sa ‘yan ajinsu suka ce ba zasu kalmashe hannu suna kallon wannan tabarbarewar ba.

A hotunan da aka dauka na yaron, an ga fuskar shi turbune babu ko alamar fara’a. Su kuwa ‘yan ajinsu a makaranta suna cikin annashuwa da nishadi don sun dauko yaron a kai don mayar dashi makaranta.

Chukwunonso Peter ne ya wallafa hotunan kuma ya bayyana cewa yaron ya ki zuwa makaranta ne duk da kuwa mahaifinshi ya biya kudin makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel