Shari’ar SIM: Hanan ta ki magana a kan zargin cin zarafin Anthony Okokie

Shari’ar SIM: Hanan ta ki magana a kan zargin cin zarafin Anthony Okokie

‘Diyar shugaban Najeriya, Hanan, ta kare kanta a kotu game da zargin da wani ‘Dan kasuwa mai suna Anthony Okolie, ya jefa mata na cewa ta toye masa hakkinsa.

Anthony Okolie ya taba amfani da lambar wayar ‘Diyar shugaban kasar, wanda hakan ya kawo aka daure shi na tsawon makonni goma, don haka yanzu ya tafi kotu.

Mista Okokie ya kai karar Hannan Buhari, da hukumar DSS da kuma kamfanin layin ta hannun Lauyansa Tope Akinyode, game da garkame shi da aka yi na wasu kwanaki.

A karar mai lamba FHC/ASB/CS/3/2020, an bukaci a tursasa wadanda ake kara (kamfanin layin, DSS da Hanan) su biya N500, 000, 000 sakamakon keta hakkin Mista Okolie.

Kamar yadda mu ka samu labari, wannan Bawan Allah ya na neman wanna kudi ne a dalilin ci masa zarfafi, da keta alfarmarsa da aka yi da kuma hana shi zuwa ko ina.

KU KARANTA: Wanda aka kama da layin wayar Hannan Buhari ya yi karin-haske

Shari’ar SIM: Hannan ta ki magana a kan zargin cin zarafin Anthony Okokie
Hanan Buhari lokacin da ta fito daga cikin jirgin fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Alkali mai shari’a Nnamdi Dimgba bai samu wani bayani daga bakin Hanan Buhari ba har yanzu. Wannan ya sa ya bukaci jin ta bakin Lauyan da ke kare ta a gabansa.

Lauyan ‘Diyar shugaban kasar ya fadawa Alkali Nnamdi Dimgba cewa duk da an zo gaban kuliya, ba su ga dalilin ba kotu amsa ko raddin wannan zargin ake yi masu ba.

Wannan martani da Bairsta ya bada ya fusata Mai shari’a Nnamdi Dimgba. “Me ka ke nufi da cewa ba ka ga dalili ba? Ana zarginka ka na cewa ba ka ga dalili ba?”

“Ko da ka fito ka ce ban yi haka ba, ba za ka iya ba? Ka na cewa ba ka ga dalilin maida martani ba. Wani irin abu ne wannan Sheriff?” Inji Nnamdi Dimgba a fusace.

Shi ma Lauyan hukumar DSS, E.E. Daobri, ya fadawa Alkali cewa har yanzu bai samu takardun da ya ke bukata daga Hedikwatar hukumar domin ya ba shari'a amsa ba.

Wanda ya shigar da karar ya koka da cewa jami’an DSS su na taso shi gaba. Wannan ya sa Alkali ya kunnen hukumar. An dakatar da shari’a sai zuwa 3 ga Watan Maris.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel