Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wata makarantar sakandire

Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wata makarantar sakandire

Ma'aikatar ilimi ta jihar Kaduna ta bayyana rufewar makarantar sakandiren gwamnati ta mata da ke Kawo bayan mummunar gobarar da ta auku. Gobarar dai ta lamushe dakunan kwanan dalibai ne har guda uku a makarantar.

A ranar Juma’a ne jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dakunan dalibai biyu ne suka kone a makarantar sakandiren gwamnatin da ke Kawo, wanda hakan kuwa ya shafi dalibai a kalla 400.

A yayin da hukumar makarantar ke ta kokarin samarwa daliban da gobara ta shafa kayan sassauci, wani dakin kwanan daliban ya kara konewa a ranar Asabar, lamarin da ya shafi dalibai sama da 1,520.

Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna ya ce an kafa kwamiti don binciko dalili ko kuma musabababin wannan gobarar.

“Mun rufe makarantar ne saboda gobara da aka yi. Zamu tabbatar da cewa an mayar da daliban zuwa kwalejin Rimi da ke jihar don ci gaba da karatunsu,” ya ce.

Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wata makarantar sakandire
Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wata makarantar sakandire
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A karo na farko, Sadiya Farouq ta yi magana kan jita-jitar auren ta da Shugaba Buhari (Bidiyo)

Yayi bayanin cewa ma’aikatar bata so rufe makarantar ba amma tilas ce ta sa hakan. Hakazalika gwamnati ba za ta so daliban su zauna gida babu karatu ba shiyasa ta ce su koma kwalejin Rimi.

Ya ce dalibai maza na kwalejin Rimin an umarcesu da su koma kowacce makaranta ce da ke kusa dasu kafin a kammala gyaran makarantar ‘yan matan.`

Malam Shehu ya yi kira ga shugabannin makarantun biyu da su hada kansu wajen tabbatar da cewa daliban sun fara samun karatu kamar yadda ya dace.

Ya ce gwamnati zata rushe dakunan kwanan da suka kone tare da dora benaye a wajen da abin ya faru.

Yayi kira ga daliban kwalejin da suka fara zanga-zanga a kan hukuncin da su kwantar da hankalinsu. Ya ce su yi hakuri da gwamnati zuwa lokacin da za a kammala ginin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel