Ana neman maganin 'Corona', wata sabuwar kwayar cuta ta sake bullowa a kasar Brazil

Ana neman maganin 'Corona', wata sabuwar kwayar cuta ta sake bullowa a kasar Brazil

Wata sabuwar cuta wacce ba a san daga inda ta bullo ba ta isa kasar Brazil wanda hakan ya matukar girgiza masu bincike. An sanya wa cutar suna Yaravirus daga Yara, wacce ta kasance wata aljanar ruwa ce mai janye sojoji zuwa karkashin ruwa don rayuwa da ita.

Masu bincike sun gano kwayoyin halitta irin na Yara kashi 99 kafin su saka mata wannan sunan tare da kiranta da sabuwar cuta.

Wannan cutar ta bullo ne a yayin da ake matukar fama da annobar Corona virus a kasar China.

COVID-19 ko kuma coronavirus ya bullo ne a kasar China a watan Disamba na 2019 kuma tuni ta halaka sama da mutane 1,000 yayin da mutane 44,500 suka kamu da ita.

DUBA WANNAN: An gano motocin alfarma 100 na biliyoyin Naira da tsohon gwamna Yari ya karkatar

An gano Yaravirus ne a watan Janairu bayan da masu bincike suka ci karo dashi a tafki Pampulha wanda yake a birnin Brazil, kamar yadda jaridar Today ng ta ruwaito.

Bayana duba kwayoyin halittar wannan cutar, an gano cewa tana da kwayoyin halitta 74 wadanda a ciki 6 kadai aka taba gani. Sauran 68 din kuwa ba a taba ganin irinsu ba.

An samu kwayoyin halittar Yaravirus ne daga wata halitta mai rayuwa a wajen danshi.

A halin yanzu dai, cutar ba ta da wani babban kalubale ga jama'a. A yanzu ba ya iya shafar dan Adam kuma ba a gano wata hanya ba, tsakanin halittar da aka same shi kadai yake iya yaduwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel