Wata sabuwa: Buhari ya san wadanda suke rike da Leah Sharibu - Kungiyar Kiristoci
- Babban limamin cocin Methodist da ke Ikeja, Bishop Steve Adegbite a ranar lahadi ya jagoranci zanga-zangar lumana
-Babban limamin ya yi hakan ne don nuna damuwarsa a kan kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma sauran kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta
- Har ila yau, wani fasto a jihar Legas din yayi kira ga shugaban kasa Buhari da ya san yadda zai yi don ya ga an sako Leah Sharibu
Babban limamin cocin Methodist da ke Ikeja a jihar Legas, Bishop Steve Adegbite a ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairu ya jagoranci jama'a don zanga-zangar lumana.
Babban limamin ya yi hakan ne don nuna damuwa a kan kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro da kasar nan ke fama dasu.
Wannan zanga-zangar ta biyo baya ne, bayan sati daya da Fasto E.A Adeboye ya jagoranci tashi tawagar don zanga-zanga a jihar Legas, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
A yayin zantawa da manema labarai, Adegbite ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauke shugabannin tsaron kasar nan saboda sun kasa shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar kasar nan.
KU KARANTA: Tirkashi: An yankewa wani hukuncin kisa ta hanyar rataya, kan ya saci waya da kwamfuta
A kan Leah Sharibu, limamin addinin Kiristan ya bukaci a sako ‘yar makarantar. Kamar yadda ya ce, Shugaban kasa Buhari ya taimaka wajen tabbatar da an sako Leah Sharibu saboda ya san wadanda ke rike da ita.
“Muna son Leah Sharibu ta dawo gida ta cigaba da rayuwarta. Su sake ta kuma su tabbatar ta dawo gida. Amintacciyar Yesu ce kuma muna son ta dawo. Muna ci gaba da yi mata addu’a. Dole ne su sako Leah Sharibu. Ya san wadanda ke rike da ita. Ya yi musu magana kuma su sako ta,” yace.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng