Jerin abinci guda bakwai da suke kawar da matsananciyar damuwa ga dan Adam - Likitoci

Jerin abinci guda bakwai da suke kawar da matsananciyar damuwa ga dan Adam - Likitoci

- Kwararrun likitoci masana lafiyar kwakwalwa sun ce saka matsananciyar damuwa a rai na kawo tabin hankali

- Sai dai kuma, saka damuwar a rai baya yaye damuwa ko ya biya wa mutum bukatar abinda ya saka a ran shi

- Akwai wasu abinci masu tarin sinadaran da ke tabbatar da fariinciki da nishadi ga dan Adam, wadannan ne ake bukatar a lazimci ci

Kwararrun likitoci masu duba ma’abota tabin hankali sun yi kira ga jama’a da su guji yawan saka kansu a matsananciyar damuwa. Hakan na daga cikin abububwa da ke haddasa tabuwar hankali.

Mutum kan fada cikin matsananciyar damuwa ne idan bashi da halin samun biyan wata bukata ko kuma samun wani abu da aka sa a gaba.

Sai dai kuma, abinda ba a sani ba shine yawan shiga damuwa baya sa biyan bukata sai dai a fada cikin hadari da yakan kai ga tabuwar hankali a lokuta da yawa.

Marissa Laliberte likita ce a kasar Amurka kuma ta bayyana cewa akwai wasu abinci da ke dauke da sinadaran da suke taimakawa wajen hana damuwa. Abincin sun hada da:

1.Ayaba

Ayaba na dauke da sinadarin ‘Vitamin B6’ wanda ke assasa samuwar sinadarin Neurotransmitter Serotonin wanda ke ingantawa tare da sa fara’a a zuciyar mutum. Karancin wannan sinadarin kuwa na sa mutum ya fada damuwa.

2. Ruwa

Shan ruwa na daga ciikin hanyoyin da suke kawo yayewar matsananciyar damuwa. Bai kuma kamata a ji kishi ba kafin a nemi ruwa ba. Karancin ruwa a jikin mutum na cutar da kiwon lafiya.

3. Beat

Beat wani abinci ne mai kama da dankalin hausa sai dai shi ja ne a ciki da waje. Ana iya cin shi danye ko dafaffe amma masana sun ce ana samun sinadarin inganta lafiyar ne idan an ci danyen.

4. Kifi

Kifin na dauke da sinadarin Omega 3 wanda ke kaifafa kwakwalwar mutum. A dalilin hakan, likitan tayi kira ga jama’a da a lazimci cin kifii domin lafiyar kwakwalwa.

5. Bakar alawar cakulet

Likitocin sun tabbatar da cewa shan cocoa rigakafi ne wajen gujewa kamuwa da cutukan hawan jini, ciwon siga, karfaffa karfin ido da sauransu.

6. Alkama

Bincike ya nuna cewa alkama na daga cikin abincin da ke sanya farin ciki domin likitoci kan shawarci matan da suka dena haihuwa da su rika cin alkama don gujewa matsananciyar damuwa.

7. ‘Ya’yan itatuwa

‘Ya’yan itatuwa kamar su tuffa, lemu, fiya, gwaiba da sauransu na sanya farin ciki sannan kuma shayi mai madara na taimakawa ba kadan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng