Arziki daga Allah: Dan gidan direban tasi a Najeriya da kasar Amurka ta bawa aikin gyaran filin jirgin sama na Chicago

Arziki daga Allah: Dan gidan direban tasi a Najeriya da kasar Amurka ta bawa aikin gyaran filin jirgin sama na Chicago

- Nosa Ehimwenman dan direban tasi ne wanda aka ba kwangilar gyara filin jirgin sama na Chicago a Amurka

- A wannan filin jirgin saman ne mahaifinshi ke dauka da sauke fasinjoji wanda da kudin ne suke rayuwa da iyalain shi

- Labarin nasarar Nosa tana da yawa don yayi wasu manyan kwangiloli masu matukar amfani da suka hada da gina asibitin jami’ar Illinois

Nosa Ehimwenman na daya daga cikin ‘yan Najeriya da suke daga sunan kasar nan a kasashen ketare. Ya fara ne a ba kowa ba don mahaifin shi matukin mota tasi ne a Amurka.

Duk da ya tashi ne a Illinois, an bashi babbar kwangila ta gyaran filin sauka da tashin jiragen sama na Chicago. Sauran kwangilolin da ya taba yi sun hada da cibiyar lafiya ta jami’ar Illinois da kuma jami’ar ita kanta.

Arziki daga Allah: Dan gidan direban tasi a Najeriya da kasar Amurka ta bawa aikin gyaran filin jirgin sama na Chicago
Arziki daga Allah: Dan gidan direban tasi a Najeriya da kasar Amurka ta bawa aikin gyaran filin jirgin sama na Chicago
Asali: UGC

Abun bada mamakin shine yadda filin jirgin saman ya zamo wajen kaiwa da kawowar mahaifin shi. A nan yake dauka da ajiye fasinjoji kuma a nan yake samun abinda zai rike iyalan shi a wancan lokacin.

KU KARANTA: An gano bidiyon shugaban dalibai na jami'a a cikin 'yan kungiyar asiri

A halin yanzu, Nosa ne shugaban kamfanin gini na BOWA, kamfanin gini ne da ya jagoranci kwangiloli sama da 25 masu matukar amfani da bada mamaki.

Nosan na tuna kalaman mahaifin shi wanda ke sa mishi kwarin guiwa mai matukar yawa. “Ni da mahaifina muna daukar fasinjoji daga wannan filin jirgin don samun abinda zamu yi rayuwa da shi. Mahaifina yana yawan fada min cewa in yi aiki tukuru tare da yin na gari. Abubuwa na gari zasu sameni,” yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel