Matsalar tsaro: Sule Lamido ya shawarci Buhari game da matakin daya kamata ya dauka

Matsalar tsaro: Sule Lamido ya shawarci Buhari game da matakin daya kamata ya dauka

Tsohon gwamnan jahar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbata ya kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya ta hanyar samar da ingantaccen tsaro a kasar gaba daya.

Lamido ya yi wannan kira ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, inda yake mayar da martani game da martanin da mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina ya mayar ma kungiyar dattawan Arewa, NEF, inda ya bayyanasu a matsayin marasa tasiri.

KU KARANTA: Akwai tambayoyi dake bukatar amsoshi game da harin Auno – Sanata Kashim Shettima

NEF ta caccaki shugaba Buhari game da abin da bayyana a matsayin gazawarsa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, hakan ya janyo martani daga fadar shugaban kasa inda ta bayyana NEF a matsayin kungiyar mutum daya kacal marasa magoya baya, wannan mutumi a nan shi ne Farfesa Ango Abdullahi.

Sai dai Lamido ya bayyana ma Buhari cewa dukkanin bayanan da NEF ta yi akwai kamshin gaskiya a cikinsu, sa’annan ya tuna ma Buhari cewa shuwagabannin NEF sune suka tsaya ma Buhari tun daga shigarsa siyasa, kuma basu taba rabuwa da shi ba duk shan kayin da ya yi a zabe.

Don haka kamata ya yi Buhari ya yi karatun ta natsu kuma ya tambayi kansa a game da menene dalilin rabuwarsu a yanzu?

“Ina kira ga shugaban kasa ya yi karatun ta natsu game da martanin da kaakakinsa Femi Adesina ya mayar ma NEF. Idan ka tuna baya yadda gwagwarmayar siyasarka ta fara tun daga APP, ANPP, CPC zuwa ACN, ire iren su Farfesa Ango da Hakeem Baba Ahmed ne suka dinga tsayawa da kai, basu taba ja da baya ba.

“Tambayar da ya kamata ka yi ma kanka a nan shi ne me yasa suka rabu da kai a yanzu da ka samu nasara, suka barka da masu ci da siyasa irinsu Femi da Garba wadanda babu abinda suke nema a hannunka sai kudi?

“Ya shugaba, dukkanin maganganun da suka yi gaskiya ne, duk da dai a matsayinka na shugaban kasa ka nuna baka san cewa matsalar tsaro ta kai haka ba har sai da kungiyoyi irinsu NEF suka fallasa. Ina kira gareka da ka karanta gargadin da Bashir Tofa ya yi ga manyan mutanen Najeriya game da matsalar tsaro a Najeriya da Afirka.” Inji shi.

Daga karshe Lamido ya karkare da cewa yana fata ba Buhari bane Janar din da bashi da Sojoji kamar yadda Adesina ya bayyana Ango Abdullahi.

“Kana da kwararrun mutane a tare da kai, ka sauraresu, nemi shawararsu, kai ne ludayinka ke kan dawo a yanzu, ka manta da Garba da Femi, cigaba da biyansu ko don sadaka, amma don Allah ka bamu tsaro.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng