Akwai tambayoyi dake bukatar amsoshi game da harin Auno – Sanata Kashim Shettima

Akwai tambayoyi dake bukatar amsoshi game da harin Auno – Sanata Kashim Shettima

Tsohon gwamnan jahar Borno, kuma wakilin mazabar Bornon ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Kashim Shettima ya yi kira ga shelkwatar tsaro ta Najeriya da ta gudanar da cikakken bincike game da harin Auno, domin kuwa akwai tambayoyi dake bukatar amsoshi game a harin.

Shettima ya bayyana haka ne cikin wata gajerar sanarwa daya wallafa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook da yammacin Talata, 11 ga watan Feburairu, inda yace tabbas an samu karuwar hare haren Boko Haram a yan kwanakin nan a wasu sassan jahar Borno.

KU KARANTA: Kotu ta wanke tsohon gwamnan jahar Neja daga zargin satar naira biliyan 1.940

“Amma babu harin daya kai na Auno muni wanda ya auku a daren Lahadi, a matsayina na Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta tsakiya, mazabar da Auno take a ciki, ina da daman da zan nemi majalisar dattawa ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike a kan harin Auno saboda akwai alamar tambayoyi da dama game da harin da suke bukatar amsoshi.

“Toh amma a matsayina na wanda ya san adadin Sojojin da suka mika rayuwarsu tare da sadaukar da rayuwarsu wajen kare al’umma jahar Borno, don haka na gwammace na yi kira ga shelkwatar tsaro wanda ita ke da hakkin kula da dukkanin ayyukan Soji da ta yi gaggawar kafa kwamitin bincike.

“Dole ne kwamitin ya kunshi mutanen kirki masu nagarta, sa’annan dole ne kwamitin ya nemi wakilai daga gwamnatin jahar Borno, jama’an garin Auno, iyakan mamatan, kungiyoyin direbobi da sauransu.” Inji shi.

Daga karshe kuma ya nemi kwamitin ta kammala aikinta cikin yan kwanaki kalilan don tabbatar da an yi adalci ga wadanda abin ya shafa tare da kare aukuwar hakan a gaba, musamman ta duba da hanyar da tafi inganci ga matafiya, kuma zata fi sauki kulawa yayin da rikicin ta’addanci, wanda muke fata zai zo karshe nan bada jimawa ba.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana bacin ransa bisa yadda Sojoji suke aiki a jahar Borno, har ma ya daka ma babban kwamandan yaki da Boko Haram tsawa saboda yadda suke cutar da jama’a a jahar.

Gwamnan ya nuna bacin ransa ne a ranar Litinin, 10 ga watan Feburairu yayin ziyarar gani da ido da ya kai garin Auno na jahar Borno inda mayakan Boko Haram suka kai farmaki suka kashe mutane fiye da 30.

A yayin ziyarar, Zulum ya zargi Sojoji da barin mutane a hannun Boko Haram, inda yace Sojojin daya kamata su samar da tsaro a Auno, amma sai ka ga sun yi tafiyarsu da an ce karfe 5 na yamma ta yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel