Bayelsa: Masu rike da mukaman siyasa sun tare wa gwamna hanya a kan hakkokinsu

Bayelsa: Masu rike da mukaman siyasa sun tare wa gwamna hanya a kan hakkokinsu

Daruruwan masu mukaman siyasa a ranar Talata sun tare hanyar shiga gidan gwamnatin jihar Bayelsa a kan bukatar Gwamna Seriake Dickson ya basu hakkokinsu.

Fusatattun masu makaman sun hana tawagar Dickson fita tare da jaddada cewa sai ya biyasu albashinsu na watannin Disamba da Janairu da sauran alawus dinsu kafin ya bar ofishinsa a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Masu bukatar hakkkokin nasu sun hana gwamnan sakata ta hanyar amfani da wutar tituna, rassan bishiya da kuma wasu manyan abubuwa don yin shinge a hanyar da tawagar gwamna za ta wuce, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Bayelsa: Masu rike da mukaman siyasa sun tare wa gwamna hanya a kan hakkokinsu
Bayelsa: Masu rike da mukaman siyasa sun tare wa gwamna hanya a kan hakkokinsu
Asali: Facebook

Masu zanga-zangar sun lalata duk tutocin PDP tare da wasu alamun jam'iyyar da ke kan shataletalen da ke kaiwa gidan gwamnatin.

Jami'an tsaron gidan gwamnatin ne suka dinga kokari wajen cire shingen da jama'ar suka yi har tawagar ta samu ficewa daga yankin.

DUBA WANNAN: Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce

Fusatattun hadiman sun saka shinge da ya rufe duk titunan da ke Onopa a Yenagoa wanda ake kaiwa zuwa gidan gwamnatin.

An gano cewa, yadda masu zanga-zangar suka dinga jifan tawagar motocin gidan gwamnatin ya tirsasa gwamnan canza hanya tare da sauran jami'an da ke tare da shi.

Dickson na da babbar matsala da dubban masu mukamai na jihar wadanda ya kora daga aiki tun a watan Nuwamba da aka sanar da sakamakon zaben jihar.

A yayin da gwamnan ya bar kwamishinoninsa tare da wasu manyan hadimansa wadanda ya nada don mika mulki, ya bukaci sauran da su koma gida su zauna.

Hakan kuwa ya tunzura masu mukamin inda suka zargi gwamnan da amfani da su tare da yasarwa. Sun bukaci ya biyasu kudadensu na watan Disamba da Janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel