Wani babban dan kasuwa ya maka rundunar sojin Najeriya a kotu

Wani babban dan kasuwa ya maka rundunar sojin Najeriya a kotu

Wani dan kasuwa a jihar Kaduna mai suna Alhaji Ibrahim Musa Gashash wanda aka fi sani da Sardaunan Matasa ya maka rundunar sojin Najeriya, shugaban rundunar, kwamandan runduna ta daya tare da daraktan hukumar jami'an tsaro ta fararen kaya a gaban babbar kotun tarayya da ke zama a Kaduna.

Alhaji Ibrahim Musa Gashash ya zargi rundunar sojin da kama shi ba bisa ka'ida ba. Sun tsinkayesa ne har gidansa inda sojin kusa 20 suka yi awon gaba da shi a watan Janairu.

Babu abinda rundunar sojin ta fada a kan shi kuma sai suka sake shi bayan kwanaki goma ba tare da sun bayyana dalilin kama shi ba ko kuma ban hakuri, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma a yayin da aka kira shari'ar a ranar Talata a kotun, sai lauyan Gashash, Sabo Garba ya bukaci da a zare shugaban hukumar jami'an tsaron fararen kaya a matsayin mai kare kansa na hudu.

Wani babban dan kasuwa ya maka rundunar sojin Najeriya a kotu
Wani babban dan kasuwa ya maka rundunar sojin Najeriya a kotu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce

Ya ce, "Wanda nake karewa na bukatar a zare shugaban hukumar jami'an tsaro ta farin kaya kuma yana fatan kotun za ta amsa bukatarsa."

Lauyan wadanda ake kara mai suna N. Nanchu ya ce zai fi kyau idan mai kara zai hado da takardar kotu mai wannan bukatar tunda wannan kotun ta kira shi.

Alkali mai sauraron shari'ar, Mai shari'a Zainab Abubakar ta bada damar a kawo wannan bukatar a rubuce. Daga nan ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu 2020 don ci gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel