Kotu ta wanke tsohon gwamnan jahar Neja daga zargin satar naira biliyan 1.940

Kotu ta wanke tsohon gwamnan jahar Neja daga zargin satar naira biliyan 1.940

Wata babbar kotun jahar Neja ta wanke tsohon gwamnan jahar Neja, Babangida Aliyu daga zargin da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ke yi masa na satar zambar kudi naira biliyan 1.4

Jaridar Guardian ta ruwaito Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, 11 ga watan Feburairu inda ta yi fatali da karar tare da sallamar tsohon gwamna Babangida Aliyu saboda a cewarta EFCC bata nuna jajircewa wajen yi da gaske game da tuhume tuhumen da take yi masa ba.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnan APC tun ba’a rantsar da shi ba

Alkalin kotun, mai sharia Mikailu Abdullahi ya bayyana cewa lauyan masu kara baya bahalartar zaman kotun, kuma ko a zaman da aka yin a karshe bai aiko da wakilinsa ba, wanda da wannan dalili ne aka dinga daga zaman har sau uku.

Bisa wannan nuna halin ko-in-kula daga bangaren EFCC ne tasa lauyan wanda ake kara ya roki kotu a kan ta yi fatali da karar sakamakon EFCC da lauyoyinta basa bin kadin shari’ar yadda ya kamata su yi, sa’annan ya nemi EFCC ta bayyana cewa ta janye karar.

Haka kuwa aka yi, daga karshe lauyan EFCC ya bayyana ma kotu cewa ya janye karar, don haka mai sharia Munkailu Abdullahi ya wanke wanda ake kara saboda rashin nuna himma daga bangaren EFCC wajen bin kadin shariar.

A wani labari kuma, Kotun koli ta tabbatar da nasarar da dan takarar gwamnan jahar Bayelsa a karkashin jam’iyyar APC, David Lyon ya samu a zaben gwamnan jahar, inda kotun ta jaddada halascin nasarar daya samu.

Kotun ta yi fatali da karar da tsohon minista a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Heineken Lokpbiri ya shigar gabanta, inda kotun ta bayyana cewa karar da ya shigar bata da tushe balle makama.

A hukuncin da kotun ta yanke a karkashin jagorancin mai sharia Inyang Okoro, kotun ta bayyana cewa kotun daukaka kara ta yi daidai a hukuncin da ta yanke inda ta yi fatali da karar da Lokpoibiri ya shigar gabanta yana kalubalantar takarar Lyon.

Kotun daukaka kara ta yanke wannan hukuncin ne bisa cewa tsohon minista Lokpoibiri ya yi nawa wajen daukaka kararsa sakamakon ya haura kwanaki 14 da doka ta tanadar na daukaka irin wannan kara, don haka ta sallami karar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel