Da dumi dumi: Kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnan APC tun ba’a rantsar da shi ba

Da dumi dumi: Kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnan APC tun ba’a rantsar da shi ba

Babbar kotun koli ta tabbatar da nasarar da dan takarar gwamnan jahar Bayelsa a karkashin jam’iyyar APC, David Lyon ya samu a zaben gwamnan jahar, inda kotun ta jaddada halascin nasarar daya samu.

Jaridar Guardian ta ruwaito kotun ta yi fatali da karar da tsohon minista a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Heineken Lokpbiri ya shigar gabanta, inda kotun ta bayyana cewa karar da ya shigar bata da tushe balle makama.

KU KARANTA: Bidiyon tsiraici: Ba zamu kori Maryam Booth daga industri ba – Kungiyar yan Fim

A hukuncin da kotun ta yanke a karkashin jagorancin mai sharia Inyang Okoro, kotun ta bayyana cewa kotun daukaka kara ta yi daidai a hukuncin da ta yanke inda ta yi fatali da karar da Lokpoibiri ya shigar gabanta yana kalubalantar takarar Lyon.

Kotun daukaka kara ta yanke wannan hukuncin ne bisa cewa tsohon minista Lokpoibiri ya yi nawa wajen daukaka kararsa sakamakon ya haura kwanaki 14 da doka ta tanadar na daukaka irin wannan kara, don haka ta sallami karar.

A ranar Juma'a, 14 ga watan Feburairu ne za'a rantsar da David Lyon a matsayin gwamnan jahar Bayelsa mai cikakken iko, inda zai amshi mulki daga hannun gwamnan PDP, Seriake Dickson.

A wani labarin kuma, akalla ma’aikata 10,000 da tsohon gwamnan jahar, Bindow Jibrilla ya dauka aiki, kuma sabuwar gwamnatin jahar a karkashin Gwamna Ahmadu Fintiri ta sallama daga aiki sun gudanar da zanga zanga a birnin Yola.

Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ya sallami ma’aikatan ne sakamakon rashin doka, ka’ida da kuma bin tsarin daya kamata wajen daukan su aiki a matsayin dalilin da yasa ta sallamesu daga aikin.

Sai dai dai a wata sanarwa daga bakin mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ta gargadi masu zanga zangar daga cigaba da gudanar da zanga zangar, saboda a cewarsa an shirya shi ne domin tayar da hankali a jahar.

“Rundunar Yansanda tana shawartar duk wani mutum ko wasu mutane dake da korafi a kan su bi hanyoyin da suka kamata wadanda doka ta shimfida wajen gabatar da korafe korafensu a maimakon tare hanyoyi suna hana jama’a wucewa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel