Asirin fasto ya tonu, bayan wani mutumi ya bayyana yadda ya kama shi yana kwanciya da matarshi da kuma 'yarshi

Asirin fasto ya tonu, bayan wani mutumi ya bayyana yadda ya kama shi yana kwanciya da matarshi da kuma 'yarshi

- Wani mutum dan asalin Najeriya ya yi tonon silili tare da fallasa ga wani fasto a kan lalata da yake da matar shi da diyar shi

- Mutumin mai zama a kasar Amurka yayi ta fada tare da tonawa faston asiri a wani bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumuntar zamani

-A tsokacin wani, yayi Allah wadai da wannan halin da wasu ke yi, ya ce dama bibul ya ce daga coci za a fara hisabi

Wani mutum dan asalin Najeriya mai zama a kasar Amurka ya fallasa faston da yake lalata da matar shi da diyar shi amma kuma yana kokarin jawo hankulan mutane a kan illar hakan, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

A daya daga cikin tsokacin da aka yi bayan wallafa bidiyon, ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar ta zamani ya ce: “Babu shakka littafin bibul yayi gaskiya. Yace daga coci za a fara hisab... Abin haushin shine yadda mutane ke zuwa coci duk ranar Lahadi tare da ikirarin cewa sun fi wadanda basu zuwa… Da yawa daga cikin masu addinin garagajiya sun fi mu,”

Ba wannan karon bane dai aka fara kama fastoci na kwanciya da matan aure ko ‘yan mata ba. A kwanakin baya wata mata tayi korafin yadda fastonsu ke zuwa har cikin gida a kan gadon mijinta yake kwanciya da ita.

KU KARANTA: An kashe matashi dan kwallon kafa a gaban iyayenshi, lokacin da ake jana'izar kakanshi

Da farko wani ciwo ne ya sameta wanda ya ja suka garzaya wajenshi neman magani tare da mijinta. Bayan ta dau kwanaki tana amfani da maganin, sai ya kare kuma ciwo ya dawo. Tuni suka kara komawa wajen faston wanda ya shawarcesu da su koma gida zai dinga zuwa da kanshi yana mata magani.

Daga nan ne fa kofa ta bude don kuwa yana zuwa har cikin gidanta koda mijin na nan sai su kulle kofa. Duk zuwanshi kuwa yana samun damar kwancya da ita a kan gadon mijinta tare da morarta yadda ya so.

Tana son sanar da mijinta mummunan lamarin amma ba ta san yadda zai dauka ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng