Yanzu Yanzu: Shugabannin PDP na zanga-zanga, sun mamaye sakatariyar EU

Yanzu Yanzu: Shugabannin PDP na zanga-zanga, sun mamaye sakatariyar EU

- Babbar jam'iyyar adawa ta dawo da zanga-zangarta kan halin da kasar da gwamnatin Najeriya ke ciki

- Jam'iyyar ta kai zanga-zangarta sakatariyar tarayyar turai da ke Abuja a ranar Talata, 11 ga watan Fabrairu

- Mataimakin Shugaban PDP na kasa (Arewa), Sanata Suleiman Nazif ne ya jagoranci zanga-zangar

Shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a safiyar ranar Talata, 11 ga watan Fabrairu, sun dawo da zanga-zangarsu na janyo hankali ga abunda suka bayyana a matsayin tabarbarewar lamura a kasar.

Zanga-zangar karkashin jagorancin mataimakin Shugaban PDP na kasa (Arewa), Sanata Suleiman Nazif, ya fara ne daga hedkwatar kamfen din jam’iyyar, Legacy House, Maitama, Abuja da misalin karfe 10:40 na safe.

Jerin motoci dauke da masu zanga-zangar ya fara tunkarar sakatariyar tarayyar Turai (EU), wanda ke a birnin tarayyar kasar. Wani jami’in tarayyar turai ne ya tarbi Nazif da sauran jami’an jam’iyyar a bakin kofa, inda daga nan aka wuce da su zuwa ginin sakatariyar da misalin 11:10 na safe.

KU KARANTA KUMA: Shugabanni na tsaron fada ma Buhari gaskiya kan ta’addanci – Shehu Sani

A wani labari na daban, mun ji cewa kalla ma’aikata 10,000 da tsohon gwamnan jahar, Bindow Jibrilla ya dauka aiki, kuma sabuwar gwamnatin jahar a karkashin Gwamna Ahmadu Fintiri ta sallama daga aiki sun gudanar da zanga zanga a birnin Yola.

Daily Trust ta ruwaito Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ya sallami ma’aikatan ne sakamakon rashin doka, ka’ida da kuma bin tsarin daya kamata wajen daukan su aiki a matsayin dalilin da yasa ta sallamesu daga aikin.

Sai dai jami’an rundunar Yansanda sun mamaye manyan hanyoyin cikin garin Yola, musamman wadanda suke kaiwa ga fadar gwamnatin jahar da majalisar dokokin jahar domin dakatar da masu zanga zangar wadanda suke nuna bacin ransu.

Wata sanarwa daga bakin mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ta gargadi masu zanga zangar daga cigaba da gudanar da zanga zangar, saboda a cewarsa an shirya shi ne domin tayar da hankali a jahar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel