Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce

Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce

- Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana debo ruwa don kashe gobara ya yadu a kafafen sada zumunta

- A wannan bidiyon kuwa, an gan ta zagaye da jami'an tsaro inda take gaggawa don kashe gobarar

- Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu a kan wannan abu inda wasu ke ta kalubalantarta

Jama'a na cewa, zama shugaba na gari dole ne mutum ya koyi yi wa jama'a hidima. Hakan ne kuwa ya faru da mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe wacce ta yanke hukuncin kashe gobara da kanta.

A cikin kwanakin nan ne aka samu gobara a makarantar sakandiren gwamnati ta jihar Kaduna wacce ta ke Kawo. Mataimakiyar gwamnan ta isa makarantar kuma an dauketa bidiyon ne yayin da take kokarin bada tallafi.

Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce
Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Innalillahi wa inna ilaihirraji'un: An halaka wani jigon APC

A bidiyon da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta, an ganta a wajen da ake gobarar da bokoti a hannu yayin da jami'an tsaro ke zagaye da ita wadanda ke ta kokarin bata kariya tare da hana mutane zuwa kusa da ita.

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta tuwita mai suna @abu-jikantanko ya wallafa bidiyon tare da jinjinawa kokarinta.

Amma kuma ra'ayinsa bai zo daya da na kowa ba, don kuwa an samu wasu da suka caccaketa da cewa na ganin ido ne da rashin dabara.

Wasu sun bayyana cewa hakan na nuna gazawar gwamnati ne ta yadda suka kasa daukar matakin gaggawa daga hukumar 'yan kwana-kwana don kashe gobarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel