Korarrun ma’aikatan jahar Adamawa 10,000 sun gudanar da zanga zanga a Yola

Korarrun ma’aikatan jahar Adamawa 10,000 sun gudanar da zanga zanga a Yola

Akalla ma’aikata 10,000 da tsohon gwamnan jahar, Bindow Jibrilla ya dauka aiki, kuma sabuwar gwamnatin jahar a karkashin Gwamna Ahmadu Fintiri ta sallama daga aiki sun gudanar da zanga zanga a birnin Yola.

Daily Trust ta ruwaito Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ya sallami ma’aikatan ne sakamakon rashin doka, ka’ida da kuma bin tsarin daya kamata wajen daukan su aiki a matsayin dalilin da yasa ta sallamesu daga aikin.

KU KARANTA: Jaruman Yansanda sun ceto mutane 4 daga hannun masu garkuwa da mutane a Abuja

Sai dai jami’an rundunar Yansanda sun mamaye manyan hanyoyin cikin garin Yola, musamman wadanda suke kaiwa ga fadar gwamnatin jahar da majalisar dokokin jahar domin dakatar da masu zanga zangar wadanda suke nuna bacin ransu.

Wata sanarwa daga bakin mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ta gargadi masu zanga zangar daga cigaba da gudanar da zanga zangar, saboda a cewarsa an shirya shi ne domin tayar da hankali a jahar.

“Rundunar Yansanda tana shawartar duk wani mutum ko wasu mutane dake da korafi a kan su bi hanyoyin da suka kamata wadanda doka ta shimfida wajen gabatar da korafe korafensu a maimakon tare hanyoyi suna hana jama’a wucewa.” Inji shi.

Shi kuma a nasa jawabin, mai magana da yawun korarrun ma’aikatan, Fasaila Baba ya musanta zargin da gwamnati ta yi na cewa ba’a bi ka’ida ba wajen daukan su aiki, inda yace an sallamesu ne kawai saboda siyasa.

Sai dai a jawabinsa, shugaban ma’aikaytan jahat, Edgar Amos ya bayyana cewa ma’aikatan da aka sallama basu kai 10,000 ba, kuma akwai matsaloli tattare da daukan nasu aiki, kuma a yanzu ma gwamnati na shirin daukan wadanda suka cancanta aiki.

“Gwamnati na shirin daukan malamai 2000 da zasu koyar a makarantun sakandari, haka zalika gwamnati za ta dauki jami’an kiwon lafiya aiki, da suka hada da likitoci, unguwan zoma da malaman jinya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel