Wanda ya lashe gasar mafi lalaci a duniya, ya tura abokinshi ya karbo mishi kyautar da aka bashi

Wanda ya lashe gasar mafi lalaci a duniya, ya tura abokinshi ya karbo mishi kyautar da aka bashi

- Wani mutumi wanda ya lashe gasar wanda yafi kowa lalace a duniya, ya tura abokinshi mahaifarsa yaje ya karbo masa lambar yabo

- Mutumin mai suna Craig Martin ya ce ba zai iya zuwa ba saboda yana bacci ne na tsawon awanni 16

- Martin an bayyana cewa ya shafe shekara uku bai fito daga gida ba sai sau daya da ya fito yaje wajen likita a asibiti

Mutane sun sami abin magana a kai a shafukan sada zumunta, bayan Craig Martin ya tura abokinshi ya karbo mishi lambar yabo a garinsa na Johannesburg, bayan ya lashe gasar mutumin da yafi kowa lalaci a duniya.

Mutumin mai shekaru 31, an bashi lambar yabo saboda kaiwa kololuwar lalaci da yayi. Kimanin mutane 200 aka gayyata wannan gasa a kasar Afrika ta Kudu.

Wanda ya lashe gasar mafi lalaci a duniya, ya tura abokinshi ya karbo mishi kyautar da aka bashi
Wanda ya lashe gasar mafi lalaci a duniya, ya tura abokinshi ya karbo mishi kyautar da aka bashi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Najeriya ce kasa ta 1 da aka fi kwankwadar barasa a nahiyar Afrika

Mutane 193 sun samu halarta. Sai kuma mutane 6 da basu samu halarta sun bayar da dalilinsu na kasa zuwa wajen taron bayar da lambar yabon. “Bani da karfin iya zuwa wajen karbar lambar yabon. Bacci nake yi sama da awanni 16 da suka wuce,” Cewar Martin da aka yi hira da shi a waya ta hanyar bidiyo.

Martin ya fito sau daya kawai daga cikin gidansa cikin shekara uku, shi ma din saboda yaje asibiti ne wajen likita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel