Mijin tace: Mata za ta yiwa mijinta saki uku saboda ya nemi irin aikin da take nema

Mijin tace: Mata za ta yiwa mijinta saki uku saboda ya nemi irin aikin da take nema

- Wata mata mazauniyar London ta garzaya gaban kotu da bukatar a tsinke igiyar aurenta da mijinta mai shekaru biyu

- Bayan mijin ya koma makaranta don karantar karatun jinya, matar ta duba hakan da yunkurin yin gasa da ita

- A wani labarin kuwa, mata ce tayi wa mijinta mugun duka bayan ya kasa yi mata ciki

Wata mata mazuniyar London wacce asalinta ‘yar Najeriya ce ta gurfana a gaban kotu da bukatar a tsinke aurenta mai shekaru biyu. Matar ta ce hakan ya biyo bayan ‘gasa’ da mijin ke son yi da ita don yana koyon irin aikinta.

Kamar yadda ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar ta tuwita mai sun @RealChuka ya wallafa kuma jaridar Within Nigeria ta gani, matar tayi barazanar raba aurensu da abokin shi ne saboda ikirarinta na cewa yana gasa da ita.

Kamar yadda ya wallafa: “Abun mamaki ne wannan da na karanta a kafar sada zumunta ta WhatsApp yanzu. Abokina ne yayi aure a watan Yuni na 2018 amma yanzu matar shi na bukatar saki. Tana zama a London ne. A cewar matar ‘A kan me zaka koma makaranta don karantar aikin jinya bayan ka san aikina kenan. So kake kayi gasa dani ko mene’ a kalamanta. Wannan wanne irin rashin kirki ne kuwa da zaka iya yi wa abokin rayuwarka?”

KU KARANTA: Bruce McConville: Mutumin da ya kone dala miliyan daya, saboda baya so ya biya tsohuwar matarshi kudin kula da yaransu

A wani labari na daban, wata matar aure ta yi wa mijinta mugun duka bayan da ya kasa yi mata ciki. Sannan kuma ta karba naira dubu dari shida da hamsin daga hannunshi.

Chita mai shekaru 32 an zargeta da cin zarafin mijinta saboda halin ko-in-kula da ya nuna ga aurensu wanda hakan yasa ya kasa yi mata ciki. Hakan yasa mijin ya kasa dawowa gida.

Matar ta fara cin zarafin mijinta ne tun a 2018 wanda hakan ya jawo mishi samun raunika daban-daban bayan ‘yan sanda sun shiga lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel