Jaruman Yansanda sun ceto mutane 4 daga hannun masu garkuwa da mutane a Abuja
Rundunar Yansandan Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja sun ceto wasu mutane hudu da miyagun yan bindiga suka yi garkuwa dasu a Abuja a ranar Litinin, 10 ga watan Feburairu.
Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa Yansansan sun ceto mutanen ne bayan wani samame dasu kaddamar a wata mafakar miyagu yan bindiga a Abuja dake Tsauni cikin garin Lambata a kan iyakan Abuja da jahar Neja.
KU KARANTA: Gwamnan Borno ya yi ma Sojojin Najeriya kaca kaca bayan harin Boko haram a Auno
Kaakakin rundunar Yansandan Abuja, Anjuguri Manzah ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin inda yace sun ceto mutanen ne bayan wani aiki na musamman da rundunar ta kaddamar.
Manzah yace an kubutar da mutanen ne bayan Yansanda sun fatattaki yan bindiga daga mafakarsu dake kan tsauni, ya kara da cewa hakan ya faru sakamakon samun kira da suka yi a kan cewa an yi garkuwa da mutane biyu daga gidansu a Gwagwalada a ranar 8 ga wata.
“Biyo bayan samun wannan kira ne Yansanda dake ofishinmu na Gwagwalada suka kaddamar da samame wanda ya tilasta ma yan bindigan tserewa tare da barin mutanen da suka sata bayan tsawon lokaci ana musayar wuta” Inji shi.
A cewarsa, sunayen mutanen biyu da aka sace a Gwagwalada sun hada da Umaru Salihu da Mariam Umaru, yayin da sauran mutanen biyu kuma da suka ceto sun hada da Zilkifilu Usman da Usman Shuaibu, wanda suka bayyana cewa a ranar 2 ga wata aka sacesu a jahar Neja.
Daga karshe kaakaki Manzah ya yaba ma kungiyar yan bijilanti da suka taimaka ma Yansanda wajen kai samamen.
A wani labarin kuma, rundunar Sojan kasa ta bayyana cewa ta ceto wasu dalibai guda uku daga hannun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram bayan wata zazzafar gumurzu da musayar wuta da suka yi da juna a jahar Borno.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito babban kwamandan rundunar Soja dake yaki da yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ne ya bayyana haka yayin da yake mika daliban uku ga iyayensu.
A jawabinsa, Adeniyi yace daliban sun hada da yan mata biyu dake karatu a kwalejin gwamnatin tarayya ta yan mata dake Maiduguri, FGGC Maiduguri, sai kuma wani namiji daya wanda aka yi garkuwa dasu a kan hanyar Maiduguri Gubio a ranar Lahadin da ta gabata.
Adeniyi ya bayyana sunayen daliban kamar haka; Wommi Laja, Ammo Laja da kuma Kingi Laja, inda yace sun samu nasarar kubutar dasu ne bayan musayar wuta tsakanin yan ta’adda da wani hazikin Soja Laftanar Kanal Idris Yusuf, kwamandan Bataliyan Soja a Gubio.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng