Sojoji sun ceto wasu dalibai mata na FGGC Maiduguri daga hannun Boko Haram

Sojoji sun ceto wasu dalibai mata na FGGC Maiduguri daga hannun Boko Haram

Rundunar Sojan kasa ta bayyana cewa ta ceto wasu dalibai guda uku daga hannun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram bayan wata zazzafar gumurzu da musayar wuta da suka yi da juna a jahar Borno.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito babban kwamandan rundunar Soja dake yaki da yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ne ya bayyana haka yayin da yake mika daliban uku ga iyayensu.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya yi ma Sojojin Najeriya kaca kaca bayan harin Boko haram a Auno

Sojoji sun ceto wasu dalibai mata na FGGC Maiduguri daga hannun Boko Haram
Sojoji sun ceto wasu dalibai mata na FGGC Maiduguri daga hannun Boko Haram
Asali: Facebook

A jawabinsa, Adeniyi yace daliban sun hada da yan mata biyu dake karatu a kwalejin gwamnatin tarayya ta yan mata dake Maiduguri, FGGC Maiduguri, sai kuma wani namiji daya wanda aka yi garkuwa dasu a kan hanyar Maiduguri Gubio a ranar Lahadin da ta gabata.

Adeniyi ya bayyana sunayen daliban kamar haka; Wommi Laja, Ammo Laja da kuma Kingi Laja, inda yace sun samu nasarar kubutar dasu ne bayan musayar wuta tsakanin yan ta’adda da wani hazikin Soja Laftanar Kanal Idris Yusuf, kwamandan Bataliyan Soja a Gubio.

“A ranar 9 ga watan Feburairu yan Boko Haram sun dira hanyar dake tsakanin Magumeri da Gubio a cikin motoci 15, cikin mintuna biyu suka yi awon gaba da dalibai uku, daliban na sanye da kayan makaranta, shi yasa basu yi wahalar ganewa ba.

“Ba tare da bata lokaci ba kwamandan Bataliyar Soja dake Gubio ya tattara Sojojinsa, inda suka bi sawun yan ta’addan tare da taimakon jama’an yankin da suka bashi bayanan sirri, daga karshe dai har sai da ya ceto yaran, mun yi farin ciki kwarai da gaske da ceto yaran, kuma gasu suna cikin koshin lafiya.” Inji shi.

Daga nan sai Adeniyi ya yi kira ga iyaye dasu dinga lura da yaransu, kuma ya shawarci iyaye su daina barin yaransa suna sa kayan makaranta musamman a lokacin da suke tafiya.

Da take jawabi a madadin iyayen yaran, Aisha Laja ta yaba tare da jinjina ma rundunar Soja da kuma matasa yan sa kai bisa yadda suka ceto yaran nasu, sa’annan ta yi kira ga jama’a da su cigaba da baiwa Sojoji bayanan sirri da zasu taimakesu a aikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel