Sanata Uba Sani ya yi wa wadanda suka yi gobara sha tara ta arziki

Sanata Uba Sani ya yi wa wadanda suka yi gobara sha tara ta arziki

- Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Uba Sani, ya tallafawa wadanda suka yi gobara da wasu kudade

- Dakin kwanan dalibai na makarantar gwamnati ta ‘yan mata da ke yankin Kawo a jihar Kaduna yayi muguwar gobara

- Shugabar makarantar ‘yan matan, Rakiya Isma’ail Ahmed ta jinjinawa kokarin sanatan a kan wannan tallafi

Dalibai da malaman da mummunar gobarar da aka yi a makarantar sakandiren gwamnati da ke Kawo Kaduna sun samu tallafi daga Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Sanata Uba Sani.

Legit,ng ta gano cewa Sanatan mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan, ya ba makarantar tallafin naira miliyan daya cif a ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu na 2020.

Wadanda suka samu wannan tallafin don rage zafin rashin abinda wutar ta lashe, sun hada da dattijan mata masu kula da daliban guda uku, sai kuma wasu dalibai na musamman daga jihar Borno.

Sanata Uba Sani wanda ya ziyarci makarantar da kansa, ya jajantawa yankin tare da duba yadda wutar ta lashe ginin. Ya aiko musu da kudin ne kasa da sa’o’i 14 bayan ya kai ziyarar ta hannun wasu hadimansa.

Sanata Uba Sani ya yi wa wadanda suka yi gobara sha tara ta arziki
Sanata Uba Sani ya yi wa wadanda suka yi gobara sha tara ta arziki
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: 2023: Cancanta za mu duba ba yanki ba wurin zaben dan takarar shugaban kasa - Sule Lamido

A yayin nuna jin dadin wannan tallafin, Rakiya Isma’il Ahmed, wacce ita ce shugabar makarantar, ta ce Uba Sani ya cika alkawarin da yayi wa wadanda gobarar ta shafa da kuma hukumar makarantar.

Al’ummar makarantar na mika godiyarsu ga Sanatan a kan tallafin da yayi musu tare da cika alkwarinsa. Muna fatan Ubangiji ya albarkacesa tare da yalwata masa arzikinsa,” shugaban makarantar ta ce.

Daya daga cikin dattijan matan da ke kula da dalibai, wacce ta samu tallafin mai suna Jummai Shehu, ta tabbatar da samun sakon tallafin kuma ta ce ta jinjinawa Sanatan ta yadda ya cika alkawarinsa da gaggawa. “Dama haka duk shugabanni suke wajen taimakawa masu bukata da gaggawa kamar yadda Uba Sani yayi.” Ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel