Abinda Buhari ya fada a kan Boko Haram bayan sun kai sabon hari a Borno

Abinda Buhari ya fada a kan Boko Haram bayan sun kai sabon hari a Borno

Shugaban kasa, Muhamadu Buhari, ya mika sakon jaje da ta'aziyya ga jama'ar kauyen Auno da ke kan hanyar Damaturu - Maiduguri, tare da basu tabbacin cewa gwamnatinsa ba zata taba gajiya wa ba wajen ganin ta yi maganin shaidancin kungiyar Boko Haram tare da kawo karshenta baki daya.

A cikin wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar ranar Litinin a Abuja Buhari ya Alla-wadai da harin da kungiyar Boko Haram ta kai a kan matafiya, 'farar hula', a kusa da Maiduguri.

An kashe kusan mutane 30 yayin harin tare da yin awon gaba da mata da kananan yara da dama.

Kazakika, shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ba zata bari kungiyar ta'addanci ta hana 'yan Najeriya

A cewarsa, "babu wani abu da zai dauke hankalin wannan gwamnati wajen daga sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare jama'a da dukiyoyinsu."

Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnatin jihar Borno tare da yin gargadin cewa kwanakin 'yan ta'addar na daf da karewa.

Abinda Buhari ya fada a kan Boko Haram bayan sun kai sabon hari a Borno
Buhari
Asali: Twitter

"Rundunar sojojinmu tana cigaba da karbar sabbin kaya yaki na zamani domin yakar kalubalen tsaro da muke fama dasu, tabbas zamu murkushe ragowar birbishin 'yan Boko Haram kwanan nan," a cewar Buhari.

DUBA WANNAN: Duk wata sai ya cire N500 daga asusun jiharsa na tsawon shekaru 8 - EFCC ta bankado badakalar tsohon gwamnan PDP

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa fararen hula matafiya sun rasa rayukansu yayin harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai Auno da misalin karfe 9:45 na daren ranar Lahadi. 'Yan ta'addar sun kona motocin matafiyan, wadanda suka yi jerin gwano a kan hanya.

NAN ta bayyana bidiyon yadda mayakan Boko Haram suka kona motoci da gawar mutane ya zagaya a dandalin sada zumunta ranar Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel