Zamfara: Kansiloli 5 na APC sun koma PDP

Zamfara: Kansiloli 5 na APC sun koma PDP

Biyar cikin goma sha daya na kansilolin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC na karamar hukumar Gusau da ke jihar Zamfara sun koma jam'iyya mai mulki ta PDP a jihar.

Wannan na kunshe ne a takardar da Yusuf Idris, daraktan yada labarai, wayar da kai da sadarwa na Gwamna Matawalle ya sa hannu sannan ya ba manema labarai a garin Gusau a ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Wadanda suka sanar da sauya shekar tasu sun bayyana hakan ne a gidan gwamnan na kan shi da ke Gusau. Sun hada da Shehu Isa na gundumar Sabon Gari, Abdulhamid Sani na gundumar Ruwan Bore, Ibrahim Kogo na gundumar Wonaka, Yahaya Aliyu na gundumar Madawaki da Shamsu Umar mai wakiltar gundumar Rijiya.

Idris ya ce kansilolin sun yanke hukuncin sauya shekar ne sakamakon tabbatuwar tsaro da kuma nasarorin da aka samu ta hanyar yaki da 'yan ta'adda da kuma manyan aiyukan ci gaba da PDP ta je musu da su.

"Tunda siyasa ci gaba ta kunsa da kuma cimma burikan masu kada kuri'a, kuma gwamnan na kokarin gyara jihar, ballantana Gusau. Jama'ar mazabarsu zasu yi alfahari matukar suka gane suna cikin tafiyar alherin," takardar ta kara da cewa.

DUBA WANNAN: An kama wani mutum da wuka yana niyyar kashe Donald Trump a fadar gwamnatin Amurka

"Dukkan kansilolin da aka gabatarwa gwamnan sun tabbatar da cewa zasu yi biyayya ga mulkin Matawallen Maradun ta yadda za a ci gaba tare.

"A yayin jawabi a taron, shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Gusau, Alhaji Sanusi Sarki, ya kwatanta sauya shekar kansilolin da alamar kwarin guiwa da imanin da jama'a suka yi da gwamnatin PDP din karkashin Gwamna Bello Matawalle," Yusuf ya ce.

Ya ce gwamnan ya mika godiyarsa ga kansilolin da suka koma jam'iyyar kuma ya ce za a yi tafiyar dasu tamkar tsofaffin 'yan jam'iyya.

Gwamnan yayi kira ga sabbin shigan da su dinga bashi shawara mai amfani ta yadda zai tafi da gwamnatin jihar.

Ya tabbatar da cewa ba zai yi kasa a guiwa ba wajen kawo romon damokaradiyya ga jama'ar jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel