An kama wani mutum da wuka yana niyyar kashe Donald Trump a fadar gwamnatin Amurka
- Jami’an ‘yan sandan kasar Amurka sun kama wani mutum da ake zargi da yunkurin kashe shugaba Donald Trump
-Jami’an ‘yan sandan sun kama Roger Hedgpeth mai matsalar kwakwalwa da wuka yana yunkurin kashe Trump
- An kama Hedgpeth da bindiga kirar Pistol a wajen fadar shugaban kasar a ranar Asabar, 8 ga watan Fabrairu
Jami’an ‘yan sandan kasar Amurka na farin kaya sun kama wani mutum mai shekaru 25 mai suna Roger Hedgpeth. Roger dai dan asalin Brandon ne na Florida kuma an kama shi ne da wuka wacce ya dauka da niyyar kashe shugaban kasa Donald Trump.
Jaridar Dailymail ta ruwaito cewa ‘yan sandan sun kama mutumin ne a farfajiyar fadar shugaban kasar Amurkan wacce aka kira da “White House” a ranar Asabar, 8 ga watan Fabrairu.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Gwamnan Gombe ya dakatar da shugaban hukumar kudin shiga ta jihar
Kamar yadda ‘yan sandan sashen suka sanar, Hedgpeth ya amsa lafinsa inda ya tabbatar da cewa kisan kai yaje yi da wukar.
Bayan kwace wukar da aka yi, jami’an sun ce an tsare shi tare da fara bashi kulawa da dubawa ga kwakwalwarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa, Hedgpeth dai da aka kama da Pistol ya gudo ne daga wani gidan mahaukata.
A wani rahoto na daban, an ji cewa Trump ya kori manyan jami’ai biyu wadanda suka bada shaida don tumbuke shi daga kujerarsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng