Gwamnan Gombe ya dakatar da shugaban hukumar kudin shiga ta jihar

Gwamnan Gombe ya dakatar da shugaban hukumar kudin shiga ta jihar

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya dakatar da shugaban hukumar kudin shiga ta jihar. A takardar da babban mataimakin gwamnan na musamman, Isma'ila Uba Misilli ya fitar, ya ce ana bukatar dakataccen shugaban, Salisu Adamu Dukku da ya mika ragamar hukumar ga Abubakar Inuwa Tata, shugaban Fiscal Responsibility Commission.

Kamar yadda takardar ta bayyana, shugaban hukumar, Salisu Dukku da wasu ma'aikata uku; Abubakar Magaji Difa, Ismail Ishaq da Umar Shamaki Tula, su gaggauta kai kansu ofishin sakataren gwamnatin jihar don umarni na gaba.

Amma kuma, Sadiq Abubakar, Sulaiman Adamu da Mohammed Usman Bello an umarcesu da su gaggauta mika karagar mulkin sashensu ga mataimakansu sannan kuma su garzaya ofishin shugaban ma'aikatan jihar don samun umarni na gaba.

Gwamnan Gombe ya dakatar da shugaban hukumar kudin shiga ta jihar
Gwamnan Gombe ya dakatar da shugaban hukumar kudin shiga ta jihar
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Zuwa da mata zauren majalisa: Mahaifina ya mutu ya bar 'ya'ya fiye da 40 - Hon. Alasan Doguwa

Amma kuma takardar ba ta sanar da dalilin dakatar da ma'aikatan hukumar kudin shigan ba kasa da watanni bakwai da aka basu mukaman.

Toh sai dai wata majiya da ta bukaci a sirranta ta kuma mai karfin, ta ce hakan na da nasaba da rashin kwazo tare da zarginsu da rub da ciki a kan kudaden da hukumar ke samarwa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

"Bayan rashin wani abin arziki ta fannin kudin shiga tun bayan da aka nada su a watanni bakwai da suka gabata, ana zarginsu da waddaka tare da watanda da kananan kudaden da hukumar ta samu," majiyar ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel