Matsalar tsaro: Yan Achaba 186 da babura 320 sun fada komar Yansanda a Katsina

Matsalar tsaro: Yan Achaba 186 da babura 320 sun fada komar Yansanda a Katsina

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Katsina ta sanar da kama wasu babura guda 320 tare da yan Achaba 186 biyo bayan kaddamar da dokar haramta aikin babur a cikin garin Katsina a tsakanin wasu lokutta da gwamnatin jahar ta kirkiro.

Punch ta ruwaito wannan doka dai ta fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Janairu domin taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka cigaba da ta’azzara a jahar. A yanzu dai gwamnati har ta gurfanar da yan Achaban gaban kotu saboda karya dokar.

KU KARANTA: Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka, inda yace suna cigaba da gudanar da bincike a kan kyasa kyasai 134 daya danganci karya dokar haramta achaba a Katsina.

“Ya zama wajibi a kan rundunar ta sanar da jama’a game da cigaban da aka samu a kokarinta na yaki da miyagun ayyuka a jahar tare da bayyana musu tasirin da wasu matakan da rundunar take dauka game da hakan.

"Musamman game da ayyukan yan bindiga da dokar haramta zirga zirgar babur a tsakanin 7 na yamma zuwa 6 na safe. Zuwa yanzu mun kama babura 320, kuma mun gabatar da mutane 186 gaban kotu yayin da muke cigaba da bincike a kan wasu mjtane 134.” Inji shi.

A wani labari kuma, Shugaban kwamitin majalisar dattawan Najeriya mai kula da rundunar Sojan kasa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa a yanzu dakarun rundunar Sojan kasa suna bin mayakan yan ta’addan Boko Haram har zuwa sansanoninsu domin gamawa dasu.

Ndume ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar asabar, inda yace Sojojin sun samu kwarin gwiwa ne biyo bayan umarnin da rundunar Sojan kasa ta bayar na su dinga kaddamar da hare hare a kan yan ta’addan ba sai sun jirasu ba.

Ndume yace a yan kwanakin da suka gabata ma Sojoji sun mayar da biki a kan wasu yan ta’adda a Kalla dake kusa da Dabua, inda suka yi ma yan ta’addan rakiyar Kura har zuwa sansanoninsu, inda suka lalatasu gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel