Matsala ce mai nasaba da tsarin kundin mulki - Ganduje ya yi magana a kan Sarki Sanusi II

Matsala ce mai nasaba da tsarin kundin mulki - Ganduje ya yi magana a kan Sarki Sanusi II

Gwamna Abdullahi Umar ganduje na jihar Kano, ya ce barakar da ke tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi II da gwamnatin jihar Kano za a iya shawo kanta hankali kwance saboda kundin tsarin mulki ta shafa.

Ganduje ya sanar da hakan ne a ranar Juma’a a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Ganduje ya jagoranci wasu wakilai ne daga jihar Kano din don mika godiyarsu ga Shugaba Muhammadu Buhari a kan aiyukan ci gaba da na habaka rayuwa da aka kai jihar.

Matsala ce mai nasaba da tsarin kundin mulki - Ganduje ya yi magana a kan Sarki Sanusi II
Matsala ce mai nasaba da tsarin kundin mulki - Ganduje ya yi magana a kan Sarki Sanusi II
Asali: Twitter

Wakilan jihar kano din sun kunshi Sarki Bichi, Aminu Ado Bayero, manyan masu ruwa da tsaki da kuma wakilan jihar na gwamnatin tarayya da suka hada da shugaban masu rinjaye na majailsar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, da sauransu.

DUBA WANNAN: Sarkin Musulmi ya yi gargadi a kan rundunar tsaro ta Shege-Ka-Fasa

A lokacin da aka tambaya dalilin da yasa Sarki Sanusi baya cikin wakilan kuma me zai kawo karshen barakar da ke tsakanin gwamnan da sanannen basaraken, sai Gwamna Ganduje ya ce, “Kun yi tambayoyi masu matukar sarkakiya amma bari in fara amsa ta farko. Muna da sarakuna masu daraja ta farko har guda biyar a jihar, kuma Sarkin Bichi na daya daga ciki. Ba zai yuwu in taho da dukkan masarautun ba.”

“Tabbas akwai kwamitin dattijan Arewa da suka shiga sasanta tsakanin gwamnatin jihar Kano da kuma Sarkin. Mun hadu da kwamitin kuma har yanzu muna tattaunawa ne. Abinda kadai zan iya cewa kenan. Matsalar da ke tsakani kuwa a kundin tsarin mulki ne kuma za a shawo kanta a saukake.” Cewar Ganduje.

A kan sabon kungiyar tsaro ta Arewa mai suna ‘Shege ka Fasa’, Gwamna Ganduje ya ce jihar za ta ci gaba da amfani da tsarin tsaronta na baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel